Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Masu Koyarwa Shida Da Chelsea Ta Ke Zawarci?

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta dukufa wajen ganin ta maye gurbin mai koyarwa Mauricio Sarri wanda ya bayyana cewa yanason barin kungiyar domin komawa koyar da kungiyar Jubentus dake kasar Italiya a kakar wasa mai zuwa.

Sarri dai yaji dadin zaman Chelsea inda ya jagoranci kungiyar ta kammala kakar wasan data gabata a mataki na uku sannan kuma ya lashe gasar cin kofin Europa da kungiyar bayan sun doke Arsenal a wasan karshe a birnin Baku dake kasar Azerbaijin.

Tuni dai ka kammala tattaunawa tsakanin mai koyarwa Sarri da kuma shugabannin Juventus akan komawarsa kungiyar sai dai Chelsea tana fatan kafin ta bashi dama domin ya bar kungiyar sai ta dauki sabon mai koyarwa.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa da yawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da kuma ragowar masu koyar  da kungiyar a yanzu suna fatan kungiyar ta dauki tsohon dan wasanta, Frank Lampard domin ya maye gurbin Mauricio Sarri, wanda zai koma Juventus.

Har ila yau Chelsea tana tunanin maye gurbin Sarri da Maximiliano Allegri, wanda zai bar Juventus sai kuma kociyan kungiyar kwallon kafa ta Wolves, Nuno Espirito Santos, dan kasar Portugal.

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Ajax, Eric Teng Haag shima yana cikin sunayen da Chelsea take tunani sai kuma kociyan kungiyar kwallon kafa ta Watford, Javi Gracia, shima dan Portugal.

Sai kuma Steve Holland, tsohon mataimakin kociyan kungiyar, wanda shima yake cikin masu koyarwar da ake zargin zasu iya nema kafin a fara kakar wasa mai zuwa duk da cewa kungiyar bazata siyi sababbin ‘yan wasa ba sakamakon dakatarwar da hukumar kwallon kafa ta duniya tayiwa kungiyar bayan da aka ka ma su da laifin siyan matasan ‘yan wasa ‘yan kasa da shekara 18 ba bisa ka’ida ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!