Connect with us

LABARAI

Ma’aikatar Aikin Gona Da Albarkar Kasa Ta Jihar Jigawa Ta Gudanar Da Taron

Published

on

Ma’aikatar aikin gona da albarkar kasa ta jihar Jigawa ta gudanar da taron koyi ka koyar ga na yini biyu ga masu ruwa da tsaki kan sabon shirin gwamnatin jiha na noma dan riba na shinkafa

Babban sakataren maaikatar aikin gona ta jiha Alhaji Gambo Yahaya ya sanar da hakan jim kadan da kammala taron bita a dakin karatu na jiha.

Yace an shirya taron bitar ne domin horasa da malaman gona kan sabbin dabarun aikin gona na shinkafa domin samun nasarar shirin noman cluster na shinkafa

Alhaji Gambo Ibrahim Aliyu yace ana sa ran wadanda aka koyar zasu koyar da sauran manoma idan sun koma wuraren aiyukansu

Yace wadanda aka koyar sun hadar da malaman gona da daraktocin shiyya na hukumar JARDA da sauran masu ruwa da tsaki kan aikin gona

Alhaji Gambo Ibrahaim Aliyu yace mahalarta fiye da tamanin ne suka samu horan na kwanaki biyu

A jawabinsa wakilin hukumar sassakawa yace shirin na sassakawa Global ya kawo sabbin hanyoyin noma na zamani domin samun Karin abinchi

Inda kuma ya yabawa gwamnatin jihad a maaikatar aikin gona da kuma JARDA bisa kokarinsu na bunkasa aikin gona inda ya yi alkawarin cigaba da tallafawa jihar nan ta bangaren aikin gona.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!