Connect with us

LABARAI

Mu Na Zaune Lafiya Da Kabilu A Ibafo Ta Ogun – Sarkin Hausawa

Published

on

Sarkin al’ummar Hausawa mazauna unguwar Ibafo da ke karamar hukumar Obafemi Owode ta jihar ogun wadda ta ke makwabtaka da jihar Legas, Alhaji Ahehu Danyaro Usman Ibafo, ya bayyana cewar su na zaune lami lafiya tare da sauran kabilun da su ke zaune tare da su a unguwar Ibafo.

Sarkin al’ummar Hausawan ma zauna garin Ibafo ya fadi haka ne a garin na Ibafo jim kadan bayan sun kammala taron su da sauran kabilun yankin, domin tattaunawa a game da al’amuran da za su kara kawo zaman lafiya a tsakaninsu.

Tunda farko sarkin ya nuna bukatar da ke akwai a wurin taron ga wadan nan al’ummomi guda biyu al’ummar Hausawa da Yarabawa kai har da sauran kabilu mazauna wannan yanki na Ibafo da su cigaba da zaman lafiya a junansu, domin karin samun dauwamammen zaman lafiya mai dorewa a tsakaninsu da sauran kabilu mazauna wannan yanki da Najeriya bakidaya.

Sannan ya cigaba da nuna farin cikinsa ga al’ummar Musulmin Nijeriya bisa ga damar da Allah ya ba su ta kammala gudanar da azumin wannan shekarar, kamar yadda tsarin shari’ar addinin Musulunci ya umarci al’ummar Musulmin su yi akowace shekara.

Sannan ya kara cigaba da umartar sarakunan al’ummar Hausawa mazauna jihar Ogun da Legas da su cigaba da hada kawunan junansu tare da koya wa mabiyan nasu al’adun Malam Bahaushe na neman zaman lafiya a wajan guda nar da har kokin sana’o’in su da sauran al’amuran da su ka shafi ra yuwarsu ta yau da kullum sannan yakara cigaba da yabama al’ummar Hausawan unguwarsa ta Ibafo tare da Yarabawa mazauna wannan yankin da sauran kabilun cikin unguwar a kokarinsu na cigaba da zaunawa lafiya a kowane lokaci.

Sannan kuma a cewarsa ko wani abu ya taso na tsawatarwa gabadaya su ke yi, inda ya kara da cewa, wannan ya nuna ma sa cewar, akwai zaman lafiya a tsakaninsu da kuma sauran kabilun bakidaya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!