Connect with us

KASUWANCI

Mutane 5,000 Da A Ke Bi Bashi Sun Canza Matsuguni – AMCON

Published

on

Hukumar kula da kadarori ta kasa (AMCON) ta sanar da cewar sama da mutane 5,000 da ake bi bashi sun boye wasu kuma sun canza wuraren zaman su.

Gwamnatin tarayya ce ta kafa hukumar a shekarar 2010 don tattra bashi daga banuna domin tabbatr da kawo daidai a fannin hada-hadar kcibiyar kudi.

Babban Manajin Daraktan hukumar Ahmed Kuru ne ya sanar da hakan a taron manema labara a Jihar Legas a ranar juma’ar data gabata , inda yace, hukumar ta sayi bashi da ya kai 14,000 kuma ta karbo wannan kudin ne don sayen bashin da kuma mu na kokarin muga mun mayar da wannan bashin.

”Ahmed ya bayyana cewar, akwai da yawan su da suka ki biyan bashin domin basu da niyyar biya kuma mafi yawancin sun boye zan iya cewa kusan su sama da 4,000 zuwa 5,000 da ake bi bashin, sun boye don kar su biya bashin da ake binsu wasun su kuma sun canza matsugunan su.

A cewarsa, buyar tasu baza ta haifar masu da wani da mai ido ba, domin muna shirin yin Magana dahukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC“. Ya kara da cewa, aro kudi ba laifi bane, dole ne mu ranto kudi daga bankuna, amma mayar da bashi sai kuma ya zama wata matsala.

Ya sanar da cewar, dimbin baya nan da huumar take yin amfani dasu, ta samo su ne daga cibiyoyin hada-hadar kudi.

A cewarsa, babban bayani da ake bukata shine matsugunin mai karbar bashi in har ana son a karbo bashin da aka ci, mun sayo bashi na 14,000 wannan kuma ba karamin kudi bane. Acewar sa, a bisa kididdigar da muka yi ta nuna cewar akawai kimanin kasuwanci guda 350 da suka kai kimanin kashi 85 bisa dari.

Wadan da kuma aka iya ganowa sun kai 350 wasu kuma sun canza matsugunai. Ya kara da cewa mutane da dama sun koma jihar Legas da Abuja saboda matsalar kudi da aka shiga daga shekarar 2008 zuwa shekarar 2009, inda ya yi nuni da cewar akwai bukatar a yi amfani da na’urar zamani don gano inda suka koma da zama.

Ya bayyana cewar hukmra sa tana da ma’aiakta da basu wuce 400, inda hakan zai yiwa wannan adadin wuya wajen gano kasuwanci sama da14,000.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!