Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Na Shiga Kungiyar Asiri Ne Saboda Saurayina – ’Yar Shekara 14

Published

on

Wata ‘yar shekara 14 ta bayyana wa ‘yan sanda a Jihar Legas cewa, ta shiga kungiyar asiri ne saboda saurayinta. Yarinyar wacce a ka sakaye sunanta ta kara da cewa, saurayinta dan kungiyar asiri na Eiye Confraternity. Lokacin da ya zama mamba, sai ya zama dan leken asiri.  Ta bayyana hakan ne lokacin da ‘yan sanda su ke gurfanar da ita jiya a Legas tare da sauran ‘yan kungiyar asiri. Ta ce, “lokacin da mu ka fara soyayya da shi, ban san cewa shi dan kungiyar asiri ba ne.  Sai da mu ka dauki tsawan lokaci kafin na ga ne. Saboda soyayya sai na zama ‘yar kungiyar asiri.

“Tun lokacin da na shiga cikin kungiyar, ban je gida ba. Ina zaune da saurayina a cikin gidan iyayen shi.

“Bayan kungiyar ta gama nazari a kaina na tsawan lokaci, sai ni ma na zama ‘yar leken asiri. Aikina shi ne, in dunga lura da ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro. Sannan kuma ina mu su abinci.”        

Haka kuma, an cafke wani mutum mai suna Omidele Yusuf dan shekaru 41, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban kungiyar asiri na Eiye Cultists. Wanda a ke zargin ya bayyana cewa, ya sake zama mamba a kungiyar asiri na Eiye Confraternity ne, tun lokacin da a ka sake shi daga gidan yari a shekarar 2014. Wannan ya zo ne, bayan da ‘yan sanda su ka dage a kan cewa ya na da tuhuma a kansa. Yusuf ya ce, “an daure ni ne a gidan yari a shekarar 2012, bisa laifin kisan kai. A gidan yarin ne na hadu da fasto wanda ya ke yi min wa’azi. Ya canza min rayuwa mai inganci. Lokacin da na fito, na bayyana wa kungiyna cewa, na zama mutumin kwarai.

“Tun lokacin da na fito daga gidan yari, ina taimaka wa ‘yan sanda da kuma ‘yan kungiyar sa-kai wajen cafke ‘yan kungiyar asiri da ke Ikorodu, duk lokacin da su ke yin rikici. A arangamar kwananan ne ‘yan sanda su ka cafke ni. “An kashe wani tsohon mamba a gaban budurwarsa. Na je wurin tare da abokanaina domin samun bayanai. A lokacin ne ‘yan sanda su ka damke ni.

“Sakamakon arangamar ‘yan kungiyar asiri masu hamayya da juna, ya janyo kashe-kashen a yankin Ikorodu ranar Alhamis da Juma’a. Ban san komi ba a kan wannan rikici, sannan kuma ban san dalilin da ya sa ‘yan sanda su ka damke ni ba.”

An dai cafke wanda a ke zargin ne a yankin Ikorodu.         

Kwamishinan ‘yan sandar jihar, Zubairu Muazu ya bayyana cewa, “wanda a ke zargin tare da kungiyarsa ana da tuhuma a kan su. Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 15 a cikin kwana biyu. “Mun zo wannan wuri ne, domin mu kaddamar da sintiri na musamman. Wanda zai kawo karshen ayyukan kungiyar asiri. Mu na da bayanai a kan ayyukan ‘yan kungiyar asiri da kuma wasu laifuka a cikin wata shida.”

Ya kara da cewa, a cikin watan Fabrairun shekarar 2019, lokacin da ya fara aiki a matsayin shugaban ‘yan sandar jihar, ‘yan sanda sun damke mutum 202 wadanda a ke zargin ‘yan kungiyar asiri ne. Kwamishin ya ce, za a gurfanar da wadanda a ke zargin duka a kotu. Ya kara da cewa, “mun kwato muyagun makamai har guda 54.   

Sannan mun kuma cafke  mutum 105 wadanda a ke zargin ‘yan fashi da makami ne tare da masu garkuwa da mutane har guda bakai. Rundunar ‘yan sanda ta samu nasarar damke mutum 93 wadanda a ke zargi da fashi da makami, a wurare daban-daban da ke cikin jihar.

“Dakile ayyukan ‘yan kungiyar asiri ya na da matukar muhimmanci. Za mu yi amfani da dabaru na musammam wajen dakile ayyukan kungiyar asiri a jihar. Za mu hada kai da kugiyoyi tare da masu ruwa da tsaki a makarantu, makwabta da kuma ‘yan jarida. “Mun samar da kwamitin ‘yan sanda na dalibai a jami’o’i, wanda su ka shafi dukkan kungiyoyin shugaban dalibai da kuma wasu shugabannin dalibai.

“Mun lura cewa, an samu karuwar ayyukan kungiyar asiri a cikin watan da ta gabata. Mun sake samar da wasu dubaru, domin dakile wannan mummunar aika-aikan. “Mun kara karfafa rundunar ‘yan sanda masu yaki da ayyukan ‘yan kungiyar asiri, ta yadda za ta gudanar da aiki kamar yadda ya kamata. Za mu damke ‘yan kungiyar asiri a jihar, sannan mu gurfanar da su a gaban kuliya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: