Connect with us

WASANNI

Oblak Na Son Komawa Manchester United

Published

on

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, John Oblak ya bayyana aniyarsa ta komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United bayan da mai tsaron ragar shima ya fara shirin barin kungiyar a wannan lokacin.

Atletico Madrid ta kammala kakar wasan data gabata a mataki na biyu a gasar laliga sai dai duk da wannan kokari da kungiyar tayi wasu daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar sun shirya barin kungiyar bayan da dan wasa Griezman ya fara bayyana cewa bazai kasance a kungiyar ba a kakar wasa mai zuwa.

Shima dan wasa Diego Godin tuni ya bayyana barin kungiyar yayinda kuma kungiyar ta siyar da Lucas Hernandez, dan kasar Faransa zuwa kungiyar BayernMunchen sai kuma Felipe Luiz wanda shima yabar kungiyar tare da dan kasar Sipaniya, Juanfran.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana Oblak yana tunanin cewa kungiyar ba za ta tabuka wani abin kirki ba a kakar wasa ta gaba saboda duk shekara basa iya cin wani kofi kuma kungiyar babu wani shiri da takeyi na ganin ta rike manyan ‘yan wasanta.

Tuni daman aka alakanta mai tsaron ragar, dan asalin kasar Slobenia da komawa kungiyarn Manchester United bayan da mai tsaron ragar ya kasance daya daga cikin manyan masu tsaron ragar da duniya take ji dasu a wannan lokacin.

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ce dai take zawarcin mai tsaron ragar sai dai yafi son komawa Manchester United saboda haka dole sai Manchester United ta fasa banki domin biyan fam miliyan 106 domin daukar mai tsaron ragar, mai shekara 26 a duniya.

Mai tsaron raga Dabid De Gea ne dai yake son barin kungiyar wanda tuni aka danganta komawarsa kungiyar kwallon kafa ta PSG sai dai Manchester United bazata siyar dashi ba har sai ta samu wanda zai maye mata gurbinsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!