Connect with us

WASANNI

Sakon Manchester Ga Madrid: Pogba Ba Na Sayarwa Ba Ne

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sanar da kungiyar Real Madrid cewa dan wasanta na tsakiya, Paul Pogba bana siyarwa bane bayan da dan wasan ya bayyana cewa yana fatan bugawa Real Madrid wasa a kakar wasa mai zuwa.

Pogba mai shekara 26 a duniya ya kammala kakar wasan data gabata da kwallaye 16 inda kuma ya taimaka aka zura kwallaye 11 cikin wasanni 47 daya bugawa kungiyar wanda hakan yasa yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a kungiyar.

Sai dai a karshen kakar data gabata kokarin dan wasan tsakiyar ya ragu wanda sakamakon haka yasa kungiyar ta kammala gasar firimiya a mataki na shida akan teburin gasar firimiya kuma bazata buga gasar cin kofin zakarun turai bana shekara mai zuwa.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane dai ya tabbatar da cewa yanason yayi aiki da dan wasan yayinda shima ya nuna cewa yana fatan mafarkinsa na bugawa Real Madrid wasa ya kasance gaskiya nan gaba kadan.

Sai dai kamar yadda wasu rahotanni daga kasar Ingila suka bayyana kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta bayyanawa Real Madrid cewa dan wasan nata wanda ya lashe kofin duniya a shekarar data gabata da kasar Faransa ba na siyarwa bane akan kowanne farashi.

Itama tsohuwar kungiyar dan wasan wato Jibentus ta bayyana aniyarta ta sake siyan dan wasan wanda ya koma Manchester United a shekara ta 2016 akan kudi fam miliyan 89 wanda hakan yasa har yanzu babu wanda ya kai dan wasan tsada acikin tawagar kungiyar ta yanzu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!