Connect with us

RA'AYINMU

Shekara Kwana Ce!!!

Published

on

Kamar yau a ka rantsar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mafi yawan gwamnonin jihohin kasar a shekara ta 2015, amma kwanci-tashi har ga shi sun kammala zagayen zangonsu na farko na shekara hudu rigis! Wasunsu kuma da ma a zango na biyun su ke. Don haka sun kammala zagayensu duka biyun har sun sauka daga ranar 29 ga Mayun da ya gabata a makon jiya.

Wannan ishara ce ga mai hankali, domin idan ka dubi lamarin ta fuskar Shugaba Buhari, ya shafe shekara 12 tare da talakawan kasar su na hankoron ganin sun kwaci mulki daga hannun jam’iyya mai mulki a wancan lokaci ta PDP, to sai ga shi a 2015 ne Allah ya cika mu su burinsu. Bayan kafuwar gwamnatin ta shafe watanni shida kafin ta nada ministoci kawai, duk da shekara 12 da ta yi ta na neman mulki. Ma’ana, kashi daya bisa takwas na zangon mulkin an yi shi ne ba tare da Majalisar Zartarwa ba. Abinda hakan ya ke nufi shi ne, a tsawon wannan lokaci ba za a iya zartar da wasu muhimman ayyuka ga kasar ba, domin babu masu zartarwa.

A lokacin an yi ta jan kunne kan tafiyar wahainiya da yiwuwar kurewar lokaci, wanda ba a gane hakan ba sai daga bisani har lokaci ya fara kurewa, domin kowa ya san yadda shugaban ya zo ya kwanta jinya, wanda hakan ya sake cinye wa gwamnatin lokacinta ta hanyar haifar da jinkirin tafiyar da al’amura. Za a iya yarda da cewa, gwamnati ba ta gamsar da talakan da ta taru da shi ta kafa gwamnati ba a tsawon shekaru hudun nan da su ka shude, duk da cewa hakan ba ya nufin ba ta yi komai ba, a’a, ta yi iyaka bakin kokarinta, amma ko kusa bai kai yadda a ka yi tsammani ba.

A wannan karon ba a san me zai iya tasowa ba. Don haka ya zama wajibi ga dukkan zababbu, ba wai shugaban kasa kadai ba, a’a, har da gwamnoni, su farka, su yi karatun ta-nutsu, su gane cewa, yin sakaci da hangen tsawon shekara hudu na da yawa, zai iya haifar mu su da matsaloli. Kada su manta da yawansu sun yi sa’a da su ka sake koma wa kan gadon mulki, domin akwai wadanda ba su samu damar yi hakan ba, saboda yadda talakawansu su ka juya mu su baya a jihohinsu.

Zababbun nan su sani cewa, kamar yanzu ne shekara hudun za ta sake karewa. Don haka babban abinda ya fi dacewa su yi shi ne, tun yanzu su mayar da kai wajen sauke nauyin da ke

kawunansu. Duk karin kwana daya ya na nufin zaizayewa da karewar wa’adin mulkinsu. Sau da yawa ba za su ankara da cewa, wa’adin ya zo karshe ba, sai sun riga sun makara daga gyara kurakuren da su ka tafka.

A wannan shafin mun sha nanata cewa, zaben 2019 kamar yau ne. A yanzu ga shi har ya zo ya wuce. A takaice ma dai har an rantsar da sababbin shugabanni; kimanin watanni

kenan da gudanar da manyan zabukan kasar. To, yanzun ma 2023 kamar yau ce ga mai yawan rai. Yanzun nan za ku ji Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta fitar da sabon jaddawalin zaben 2023. Don haka lokaci ba ya jira, sai dai a jira shi!

Wadanda ke neman kujerun shugabannin nan da su ka lashe zabuka su na nan ba su hakura ba kuma su na jiran su yi amfani da wata dama ta kuskuren da wadanda su ke kai za su yi, don su kwace kujerunsu. Wasu kuma za su iya hana su dora wadanda su ka fi so gaje su, ga wadanda su ka kammala zangon mulki na biyu kenan.

Duk idan ka ji a na yin ka-ce-na-ce wajen kokarin dakile na kan mulki, don ya zarce ko ya dora wanda ya ke so, hakan ba ya rasa nasaba da yadda wanda ke kan mulkin ya gudanar da mulkinsa a cikin shekaru hudun da ke karewa. Idan har shugaba ya yi abinda ya kamata ta yadda ya kamata, to ba kasafai za ka ji ka-ce-na-ce a lokacin zabe ba. Abubuwa su ka zo da sauki cikin lusilama ta tunja-tunja wacce ba mai yawa ba ce. Amma idan shugaba ya zauna ya rashe ya na kallon shekara hudu a matsayin mai tsawo, to a nan matsalar ta ke.

Babban abin takaicin shi ne, a lokacin da giyar mulki ta bugar da su, ba su ji ba su gani, ba kuma su sauraron kowa, sai wanda zai furta abinda ya fi yi mu su dadi a cikin zuciyarsu. To, tun da farar safiya a ke kama fara! Wajibi ne zababbun shugabannin nan su nada abokan aiki da wuri, su zabo nagartattu masu amana da jajircewa, su ajiye son jiki, su yi aiki tukuru. Su gane cewa, a yanzu su ne bayin al’umma, wato manyan hadimansu.

Idan har su ka yi haka, za su iya tsira daga irin tsananin abubuwan kunyar da ya samu wasu gwamnoni a lokacin da su ke kokarin zarcewa da kuma wadanda wa’adinsu ya kare, amma su ke kokarin dora magadansu, amma hakan ya ci tura, inda har hakarsu ta kasa cimma ruwa.

Shekara kwana ce!
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: