Connect with us

LABARAI

Sojoji Sun Kama Mutum Uku Da Bindiga A Taraba

Published

on

Jami’an sojin na bataliya 93 dake barikin Ada a Takum ranar lahadi sun kama mutum uku dauke da bindiga tare da harsahe a kusa da Rafinkada a karamar hukumar Wukari a jihar Taraba.

 

Shugaban karamar hukumar Wukari na riko, honarabul Daniel Adi ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin a garin Jalingo, Adi ya ce; matasan sun nufi Rafinkada sanda sojin Nijeriya na barikin Takum suka bisu suka kama su dauke da bindiga kirat pistol tare da harsashe. Shugaban karamar hukumar ya ce ana ta kokari don kawo zaman lafiya tsakanin Jakun da Tibi na karamar hukumar Wukari da tabbatar da sun zauna lafiya da junan su.

 

‘Mun yi taron zaman lafiya a Kente wajen da aka fara rikicin wata biyuda suka wuce inda duka bangarorin biyu suka amince zasu zauna da juna lafiya.Jiya jiyan nan mutanen Tibi da Jukun sun hadu a kasuwar Kente a karo na farko tun farkon faruwar rikicin watanni biyu da suka wuce.

 

A halin yanzu an kai hari tare da kona gidaje a kauyen Utsev da Akaakase dake karamar hukumar Donga.

Mazauna yankin sun ce maharan sun shigo kauyukan nasu ta Ayu-Tsokondi dake karamar hukamar Wukari sannan suka shigo karamar hukamar Donga da misalin karfe 1 na daren Laraba. Jami’in hulda da jama’ a na hukumar ‘yan sanda, DSP David Misal ya sanar da cewa hat yanzu bai samu cikkekn rahoton akan harin ba da kuma kama mutane a karamar hukumar Wukari da Donga
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: