Connect with us

LABARAI

Ta Sace Dan Raino Daga Hannun Mai Raino A Cocin Garin Onitsha

Published

on

A ranar Lahadin nan ne aka yi zargin wata mata ta sace  yaro mai watanni 18 a wani Coci da ke Anguwar Awada, ta Onitsha, Jihar Anambra.

An bayar da rahoton sace yaron ne daga hannun mai renonsa a lokacin da ake mika sadakoki a wajen addu’a a Cocin.

An ce matar da ake zargi da sace yaron ta roki mai renon na shi ne da ta taimaka ta mika mata nata sadakar , ita kuma sai ta rike mata yaron har ta je ta dawo.

Wani mai wa’azi a Cocin wanda ya nemi a sakaya sunansa y ace, ba tare da zargin komai ba, sai ‘yar renon kuwa ta mika mata yaron, ta kuma karbi Naira 100 din ta tafi jefa mata a cikin akwatin sadakan. Dawowanta ke da wuya ta taras babu yaron babu kuma matar da ta taimakawa din.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da aukuwan lamarin.

Ya kara da cewa masu bincike na ‘yan sanda sun ziyarci wajen da abin ya faru, yana mai cewa, a yanzun haka suna bin hanyoyin da suka dace ne na ganin sun kama matar da ta gudu da yaron.

Ya ce, “A ranar 9 ga watan Yuni, 2019, da misalin karfe 2:30 na rana, wani mai suna Mista Olisachukwu Ezechukwu, wanda ke zaune a gida mai lamba 1, kan titin Orakwe close, Awada, ya kawo rahoto a ofishin ‘yan sanda na Awada, a wannan ranar, inda yake cewa, ‘yar aikin gidan shi mai suna, Ukwuoma Ruth, mai shekaru 16 da haihuwa ta tafi Coci a cikin garin Awada, tare da dansa mai suna, Master Chibuike Ezechukwu, mai watanni 18 da haihuwa.

“Wanda yake karan yay i zargin cewa a lokacin da ake mika sadaka a cikin Cocin, sai ‘yar aikin na shi ta hannata yaron na shi ga wata matar da har a lokacin ba a santa ba da take zaune a kusa da ita, ta kuma roke ta da ta taimaka ta mika mata nata sadakan na Naira 100.

“Sai dai a lokacin da ‘yar aikin na shi ta mika mata sadakan ta dawo, sai ta taras da babu matar ta gudu tare da yaron, har a lokacin kuma ba a gansu ba.”

Mohammed ya shawarci al’umma da su kula da wannan sabuwar hanyar ta satan yara, su kuma hanzarta kai rahoton aukuwan duk wani abu makamancin hakan ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su domin daukan mataki da gaggawa.

Ya kuma shawarci shugabannin Addini da su rika daukan kwakkwaran mataki a wuraren ibadunsu domin hana aukuwar irin wannan mummunan al’amarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: