Connect with us

LABARAI

Wadanda Su Ka Garkuwa Da Wata Mata Sun Nemi Fansar Naira Miliyan 10

Published

on

Wasu mahara sun nemi a basu zunzurutun kudi har naira miliyan 10 da sunan kudin fansa kafin su saki matar da suka sace mai suna, Mrs Olawumi Adeleye da karamin danta, wanda aka yi garkuwa da su a filin jirgin sama na garin Osi dake Akure na jihar Ondo.

Wasu masu bada shaida sun tabbatar da cewa maharan sun sace sune a kan hanyar su ta zuwa majami’a a ranar Lahadi da yamma.

A cewar wata majiya, kuma mutanen da suka aikata wannan laifin sun katange hanya ne da shanu, inda ita kuma tana cikin mota kirar Ledus,to daga wannan lokacin ne aka nema ta aka rasa inda ake kyautata zaton an kai ta wani waje wanda ba a sani ba.

Majiyar ta kara da cewa, “Mrs Adeleye tana dawowa daga majami’a tare da karamin danta, ba zato ba tsammani sai kawai Fulani makiyaya suka sanya shanu a bakin hanyar.A lokacin tayi kokarin kauce musu amma abin ya gagareta tayi iya bakin kokarin ta domin taga ta juya motar, sai suka kai mata hari a kan titin inda suka lalata motar ta daga bisani suka dauke ta tare da yaron nata.”

Sai dai kuma wata majiya daga bakin iyalin ta, ta fadi cewa, bayan wasu ‘yan sa’o’i, da faruwar lamarin masu garkuwar sun kira mijin ta a waya inda suka nemi a basu kudin fansa har Naira miliya goma.

“Lokacin da muka tuntubi jami’an tsaron ‘yan sanda jihar,Mista Femi Joseph, akan faruwar lamarin yace mana yanzu haka zai tura jami’an su zuwa wajen da abin ya faru domin gudanar da binciken kwakwaf.

“Mun riga mun fara gudanar da bincike a waje kuma zamu samu nasarar damke su cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.Mun kuma fara binciken kan lamarin”,Yusufu ya ce.

A ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin sarkin Osi, Oba Dabid Olajide,ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce masu garkuwar sun kama matar ne tare da danta a daidai lokacin da suke dawowa daga majami’a.

Oba Olajide ya ce, “Wannan abu ya faru ne kusa da filin jirgin sama na garin Akure, kuma an sace sune da misalin karfe 5:20 na yamma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!