Connect with us

WASANNI

Watakila Mourinho Ya Sake Komawa Chelsea A Karo Na Uku

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta fara shirye shiryen tuntubar tsohon kociyan kungiyar, Jose Mourinho, a kokarin da kungiyar takeyi na sake sabon mai koyarwa bayan da Mauricio Sarri ya bayyana cewa zai bar kungiyar.

Kawo yanzu dai har yanzu Mauricio Sarri ne kociyan kungiyar ta Chelsea sai dai tuni mai koyarwar, dan asalin kasar Italiya ya bayyanawa kungiyar cewa bazai cigaba da zaman kungiyar ba kuma ya gama kulla yarjejeniya da Jubentus.

Wasu Rahotanni sun bayyana cewa da yawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da kuma ragowar masu koyar  da kungiyar a yanzu suna fatan kungiyar ta dauki tsohon dan wasanta, Frank Lampard domin ya maye gurbin Mauricio Sarri, wanda zai koma Jubentus.

Sai dai wasu daga cikin tsofaffin ‘yan waasan kungiyar irinsu John Terry sun bayyana cewa abune mai kyau kungiyar ta bawa Lampard aikin kungiyar sai dai kuma bai taba koyar da wata kungiya a gasar firimiya ba wanda hakan zai iya zama matsala a wajensu.

Sai dai yanzu kuma an bayyana cewa Chelsea ta fara tunanin sake yiwa Mourinho Magana wanda ya lashe gasar cin kofin firimiya guda uku a Chelsea da kofin Lig guda uku da kuma kofin kalubale na FA guda daya domin ya sake komawa kungiyar karo na uku.

Tun bayan da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kori Mourinho baya koyar da kowacce kungiya sai dai a kwanakin baya an danganta dan wasan da komawa koyar da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United wadda wani attajiri zai siya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!