Connect with us

LABARAI

’Yan Bindiga Sun Sace Dalibin Jami’ar Usmanu Danfodiyo A Sakkwato

Published

on

An bayar da rahoton wasu ‘yan bindiga sun sace wani dalibin da yake a sashen  Microbiology, a shekarar karshe a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, mai suna Aliyu Maidamma, ana gab da ya rubuta jarabawar fitarsa ta farko.

Wakilinmu ya fahimci cewa, an sace dalibin ne a ranar Juma’a da yamma a kan hanyarsa ta komowa Skkwato daga hutun Sallah da ya tafi.

Dan’uwan wanda aka sacen, Ibrahim Sanni Maidamma, ya tabbatar da satan a lokacin da yake amsa waya daga wakilin namu.

Ya ce, “Lokaci na karshe da muka yi magana da Aliyu, ya ce mana yana kan hanyar komawa makaranta ne, tun daga lokacin kuma muna ta magana da shi a kan hanyar.

“Amma da wajajen karfe 3 na rana sai muka gaza samunsa a waya, na yi zaton ko don rashin kyawun layi ne, har sai lokacin da wadanda suka sace shi din suka kira yayanmu da yamma suka ce sun kama Aliyu ne.

Abin bakin ciki, Ibrahim ya ce sun kira suna neman a biya su Naira milyan 3 a matsayin kudin fansa kafin su sako shi.

“Sun fara kira ne da a kai masu Naira milyan 3 kafin su sako shi. Jimawa kadan sai wani ya sake kira yana gargadin in ba mu biya kudin ba za su kashe shi.

“Muna bakin kokarinmu na ganin sun sako shi. Komai yana hannun babban yayanmu ne,” in ji Sani, cikin raunanar murya.

Sai dai kokarin da wakilin namu ya yi na saduwa da babban yayan na su ya ci tura, domin baya amsa waya, baya kuma maido da amsar sakonnin da muka aike ma shi ta waya.

Shugaban kungiyar dalibai na jami’ar, Kwamared Faruk Barade, ya tabbatar da sace dalibin da aka yi, ya kara da cewa, kungiyar ba ta kai ga samun wata alaka da iyalan dalibin ba tukunna domin su sami cikakken bayani a kan lamarin.

“A jiya Litinin, mun kira iyalan na shi a waya. Daya daga cikin ‘ya’uwansa ya ce an umurce su da kar su yi magana a kan faruwan lamarin. Ya kuma bayar da shawarar mu jira babban yayan na su ya zo kafin mu ji wani abu daga gare su.”

Ya kuma koka a kan yawaitan satan mutanan da ake yi a cikin kasar nan.

“A gaskiya, yawaitan rashin tsaro, musamman abin da ya shafi satan mutane a kasar nan abin ya fa wuce gona da iri.

“Duba fa, dan makaranta? Nawa dan makaranta yake da shi? Wannan ai abin kunya ne a wajen gwamnati.

“Muna rokon Allah Ya tsare mana shi, Ya kuma dawo mana da shi lafiya,” in ji shi.

Shugaban sashen hukumar dalibai na jami’ar, Farfesa Aminu Mode, ya musanta masaniyar jami’ar a kan abin da ya faru din.

“Ba ni da labarin hakan. Kila iyayensa suna son su barwa kansu lamarin ne, su yi magana da wadanda suka sace shi din a kebe, ba wanda ya kawo mana kukan aukuwan hakan ya zuwa yanzun. Allah dai Ya Tsare shi,” in ji shi.

Hakanan, Rundunar ‘yan sanda ta Jihar ta Sakkwato, ya zuwa yanzun ba ta ce uffan ba a kan aukuwan lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!