Connect with us

KASUWANCI

’Yan Nijeriya Ma Su Mu’amala Da Internet Sun Karu Zuwa Miliyan 101.2 – NCC

Published

on

Hukumar sadarwa ta kasa (NCC) ta sanar da cewa, masu yin amfani da kafar Internet a Nijeriya sun karu zuwa miliyan 101.2 a cikin watan Afirilu daga miliyan 100.6 a cikin watan Maris.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin kafar adireshin ta internet ta wata-wata da masu butar bayanai suka yi watan Afirilun shekarar 2018 Abuja.

Ma’adanar bayanan hukumar ta nuna cewar, an samu karin masu bukata da suka kai yawan 613,275 a kasar nan.

A cewar hukumar ta NCC, kamfanonin layin sadarwa na Airtel da MTN, sunfi samun masu bukata a cikin watan, inda kamfanonin layin sadawar na Glo da 9mobile sune manyan da suka fi yin asara.

A bisa fashin bakin da aka yi, ya nuna cewa Kamfanin layin sadarwa na Airtel, ya samu sababbin masu yin amfani da internet da suka kai yawan 366,254, inda hakan ya sanya ya kara samun masu amfani da internet din a cikin watan Afirilu ya kai zuwa miliyan 25.842 daga miliyan 25.476 a cikin watan Maris.

A cewar hukumar, kamfanin layin sadawar na MTN, ya samu sababbin masu yin amfani da internet da suka kai 718,803 a cikin watan Afirilu, inda ya kai yawan miliyan 38.147, sabanin miliyan 37. 428 da aka samu a cikin watan Maris.

Kamfanin layin sadarwa na 9mobile kuwa, ya yi asarar 150,285 masu amfani da internet a cikin watan Afirilu, inda masu amfani dashi suka ragu da zuwa miliyan 10.847, sabanin miliyan 10.997 da aka samu a cikin watan Maris.

Ma’adanar bayanan ta kuma nuna cewa a cikin watan Afirilu kamfanin layin sadarwa na Globacom, ya yi asarar masu amfani da kafar inernet da suka kai 321,497, inda hakan yake nuna cewar, masu amfani da kafar inernet sun ragu zuwa miliyan 26.372 ada aka samu miliyan 26.693m a cikin watan Maris.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!