Connect with us

LABARAI

 ‘Yan Nijeriya Na Da Bukatar A Fito Da Hanyoyin Magance Rashin Aikin Yi- CDD

Published

on

Cibiyar ci gaban dimokradiyya ta CDD reshen Afrika ta yamma, a yau Laraba sun bayyana cewa; ‘yan Nijeriya na da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maishe da hankali akan fito da hanyoyin magance ayyukan yi, da bunkasa tattalin arziki da kuma magance matsalar tsaro a wa’adin mulkin sa na biyu.

Daraktan CDD na yankin, Idayat Hassan ta ce; a kwanan nan cibiyar ta saki abin da ta kira ‘2019 Buharimeter’ wani bincike da suka yi akan nasarorin da shugaban kasa Buhari ya samu a wa’adin mulkinsa na biyu. Hassan ta ce; rahoton na su ya nuna kirkirar hanyoyin aikin yi, bunkasa tattalin arziki, magance tsaro, da magance talauci a matsayin abin da ‘yan Nijeriya ke da bukata.

CDD sun tabbatar da cewa; abin da ‘yan Nijeriya suke da bukata a halin yanzu shi ne bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma magance matsalolin tsaro.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: