Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Sun Bankado Wata Matsafa, Sun Ceto Mutum 20 A Oyo

Published

on

Akalla mutane 20 ne rundunar ‘yan sanda ta Jihar Oyo ta ceto daga wata matsafa da ake zargi, wacce ake zargin dandalin matsafa ce da ke Anguwar Agungun, a garin Ibadan, Jihar Oyo.

Jami’an ‘yan sanda ne daga ofishin ‘yan sandan na Anguwar ta Agungun, suka bankado sirrin matsafar wacce ta fallasan asirin nata ya janyo hankulan al’umma da dama da ke kewayen yankin, bayan da jami’an ‘yan sandan suka sami wani bayanin sirri a kanta.

Mutanan da aka sami nasarar cetowan daga matsafar an same su ne a yankwane, kashi da rai, suna kuma hannun ‘yan sandan.

Mamallakin matsafar ko mai kula da matsafar wani mai suna, Alfa Oloore, kamar yanda aka fi da kiransa, tuni ‘yan sandan sun sami nasarar kama shi, suna kuma tsare da shi domin amsa tambayoyi.

A cewar wasu mazauna Anguwar, Alfa Oloore, wanda yake riya cewa shi mai bayar da maganin gargajiya ne, ya debi shekaru masu yawa yana gudanar da wannan matsafar, wacce aka jima ana shayinta.

Mazauna anguwar sun kwatanta wajen da cewa, dandalin matsafa ne da masu satar mutane, inda ake tsare da mutane ana ayyukan tsafi da su.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar, (PPRO), Gbenga Fadeyi, ya tabbatar da kama mai gudanar da matsafar da kuma ceto mutanan da ‘yan sanda suka yi.

Fadeyi, wanda Sufuritanda ne na ‘yan sanda y ace, gaskiyar cewa, ko wajen dandali ne na matsafa da masu satar mutane, bas u tabbatar da hakan ba tukunna har sai ‘yan sandan sun kamala bincikensu a kan lamarin tukunna.

Ya ce, “zan iya tabbatar maku da cewa mun kama wanda yake gudanar da wajen, inda kuma muka gano mutane masu yawa da ke tsare a wajen. Amma daga baya wasu mutane sun zo suka ce mana wai sune suka bayar da ‘ya’yayensu a matsafar, wanda a cewar su wai shi mai bayar da maganin gargajiya ne.

“A gaskiya, wasu daga cikin mutanan da muka gano a wajen suna da wasu alamomi na tabin hankali, suna yin abu kama fa ‘yan kwaya, wasu kuma gas u nan kamar mahaukata da dai makamantan hakan. Amma dai duk a halin yanzun ‘yan sanda suna kan bincike ne domin gano gaskiyar lamarin.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!