Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Damke Mutum Hudu ’Yan Kungiyar Asiri A Jihar Ekiti

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Ekiti ta samu nasarar damke mutum 4, wadanda a ke zargi da kisan kai, ayyukukan kungiyar asiri, mallakar wiwi da kuma gudanar da ayyukan da ke tada hankulan mutane. Kwamishinan ‘yan sandar jihar, Mista Asukuo Amba, shi ya bayyana hakan a garin Ado Ekiti ranar Litini, inda ya bayyana cewa, an samu nasarar cafke wadanda a ke zargin ne a wurare daban-daban a yankunan Ado Ekiti da kuma Oye Ekiti. Amba ya kara da cewa, wani wanda a ke zargi mai suna Babalola Kazeem dan shekara 33, wanda ya bayyana kansa a matsayin dan kungiyar asiri na Eiye Confratenity, an cafke shi ne bisa laifin kashe wani mutum mai suna Soji a yankin Orita Blessing cikin Okeila da ke Ado Ekiti, a cikin watan Disambar shekarar 2018, da kuma Tope Gana a yankin Atikankan da ke cikin garin Ado Ekiti a watan Junairun Shekarar 2019.   

Kwamishinan ‘yan sandar ya ce, Kazeem ya na daya daga cikin ‘yan fashin da su ka harbe wani mutum mai suna Adebayo Adeola a shagon askinsa da ke yankin Okeila cikin grin Ado Ekiti a shekarar 2018. Ya kara da cewa, wadanda a ke zargin sun farmaki wata mata wacce ta san komi a kansu a ranar 28 ga watan Mayun shekarar 2019, inda su ka sare ta a wuyarta tare da lalata mata waya, domin bata duk wata shaida a kan ayyukan da su ka aikata.

Amba ya ce, wasu wadanda a ke zargin mutum biyu, Richard da kuma Kayode ‘yan kungiyar asiri na Aiye Confraternity, an samu nasarar cafke su a yankin Oye Ekiti, wadanda a ke zargin sun hada kai wajen gudanar da ayyukansu na asiri tare da tayar da hankulan jama’a.

Wata Mata Ta Dauke Hankalin Mai Aiki Inda Ta Sace Yaro A Cocin Anambra

Wata mata ta sace wani yaro mai suna Chibueze Ezechukwu dan shekara daya da wata shida, a cocin Catholic da ke garin Onitsha cikin Jihar Anambra. Majiyarmu ta labarta mana cewa, an sace yaron ne ranar Lahadi a cocin ‘Ibah Pope Catholic Church’ da ke yankin Awada cikin garin Onitsha, lokacin da a ke gudanar da amsar kudin ibada. Wata majiya ta bayyana wa wakilinmu cewa, mai aikin ta na kulawa da yaron, amma sai barauniyar ta dauke hankalin mai aikin wajen ba ta kudin ibada, inda ta nuna mata za ta kula da yaron har ta je ta bayar da kudin.

“Matar ta bai wa mai aikin kudi ne, domin ta je ta bayar da kudin ibada, ta bukaci ta kula mata da yaron kafin da je ta dawo, lokacin da ta dawo sai ba ta ga matar da yaron ba. “Sai ta fara duba matar da yaron, inda har yanzu ba ta gansu ba. Don Allah duk wanda ya ga wannan yaro, to ya sanar wa ‘yan sanda na kusa,” in ji wata majiya.   

Hakazalika, an gano wata yarinya wacce ta bace a Awka, inda a ka gan ta, ta na tafiya a kan hanya sanye da inifom, inda a ka kai ta ofishin ‘yan sanda da ke Awka. Yarinyar mai shekaru 11, wani mutum mai suna Obinna Udeogu da ke yankin Enugwu Ukwu shi ne, ya tsinci yarinyar a ranar Litinin da misalin karfe 3.30 na rana, inda ya mika ta ofishin ‘yan sanda na garin Awka.

Da ya ke bayani a kan lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Anambra, SP Haruna Mohammed ya bayyana cewa, “Chinenye Ejike ‘yar shekara 11 an tsince ta ne da inifom din makarantar Christ Leaders International School da ke garin Awka, inda ta bace lokacin da ta ke tafiya gida daga makaranta tare da mai kula da ita Blessing Orijafor, a kusa da cocin Crace Church da ke yankin Umuokpu cikin garin Awka.

“Ita ‘yar asalin garin Ama-Owelle Amansea ce, ta na jin Turanci da kuma yaran Ibo. “A halin yanzu dai, ana kokarin yadda za a mika ta da iyayenta, domin ta koma cikin ‘yan uwanta.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: