Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Sun Kama Masu Fadan Addini Guda 21 A Legas

Published

on

Jami’an tsaron ‘yan sanda sun yi nasarar damke wasu mutane masu tada zaune tsaye wajen rikicin addini a jihar Legas,su de wadannan mutanen sun kware wajen aikata miyagun laifuffuka da sunan addini.Daga cikin wadanda aka kama din harda wani jigo a tafiyar tasu mai suna Yusuf Omidele, wanda aka fi sani da Janar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ya shaida hakan ga manema labarai cewa “Janar shugabane a wata kungiyar ta’addanci mai suna (Eiye Confraternity), an kuma yi nasarar kama shi tare da ‘yan kungiyar guda 21 a yankin Ikorodu na jihar Legas a yayin da babban jami’in ‘yan sandan ya jagorancin wani aiki mai suna Uduak Udom mai kula da ‘yan sanda, CSP.

Ya ce kama Janar tare da sauran ‘yan kungiyar guda  21 wanda aka gudanar da aikin karkashin CP Muazu da wasu masu ruwa sa tsaki wadanda suka sha alwashin kawo karshen ‘yan ta’addan masu cin hanci da rashawa a fadin jihar.

Elkana ya bayyana cewa a ranar 6 ga Yuni, 2019, da misalin karfe 10 na dare ‘yan sanda suka samu wani bayanin sirri wanda ke nuni da cewa akwai wasu mutane da suke aikata laifi, wanda a lokacin aka cim masu kuma anyi nasarar kama mutune a daga cikin su, a wajen.

Kungiyar Anti-Cultism ce tare da hadakar jami’an tsaro daga Ikprodu suke gudanar da wannan aikin.

A cewarsa, shugaban kungiyar, wanda ya kasance a jerin sunayen wadanda akama kama, Dokta Yusuf Omidele, wanda aka fi sani da Janar, an kama shine  tare da wasu mutane 20 wadanda suke yiwa kungiyar ta’addancin aiki.

Janar ya ce, “sau da yawa idan aka kama sa ana turasa zuwa kotu daga nan kuma a yanke masa hukunci zuwa gidan kurkuku.Ya ci gaba da cewa an kama shi karshe shekarar 2014 kuma ya zama babban magatakarda a cikin Yarjejeniyar Eiye.

Ya jagoranci kungiyarsa a wani harin da aka kai wa mambobin Aye, kuma an yi zargin cewa sun kashe matar daya daga cikin shugabannin su makonni da suka wuce.

‘Yan sanda da suka kama sun hada da yanci Aye da Eiye kuma dukansu sun furta kasancewa ‘yan kungiya ne. An ce mutane biyu sun mutu ne daga rikicin kabilanci kuma wasu shida sun ji rauni a wannan harin.

“Babban mummunan hare-haren da Dokar ta umarta game da masu cin hanci da rashawa na ci gaba da aiki tare da ganin kama wasu mambobin kungiya,

Kwamishinan ‘Yan sanda na jihar Legas, CP Zubairu Muazu, a ranar 7 ga Yuni, 2019, ya sadu da shugabannin gargajiya, shugabannin addini, tsoffin shugabannin jihohi, iyaye, matasa da sauran masu ruwa da tsaki a Ikorodu.

Inda su ka gana ta yadda za a samu bakin zaren yawan tashe-tashen hankula a jihar daga karshe kuma yace doka za tayi aiki ga duk wanda aka kama sa yana aikata laifin ta’addanci a jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: