Connect with us

LABARAI

‘Yar Shekara 17 Ta Kashe Kanta Saboda An Saki Mahaifiyarta A Kano

Published

on

Wata matashiya ta kashe kanta a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, wacce ake zargin takaicin sakin mahaifiyarta da mahaifinta ya yi ne ya sa ta aikata hakan.

Marigayiyar mai suna Halimatus Sadiyya ta mutu ta na da shekara 17, kuma daliba ce a makarantar sakandare dake unguwar Tudun Murtala, karamar hukumar Nasarawa.

Bayanan da ke fitowa daga bangaren iyayenta na nuna cewa takaici ne ya rufe Sadiya bayan mahaifinta ya saki mahaifiyarta, har ta gwammace ta bar duniya maimakon ta ci gaba da ganin abun bakin ciki.

Wani dan sabani ne ya shiga tsakanin ma’auratan biyu, wanda ya jawo muguwar rashin jituwa, hakan har ya kai ga mahaifin Sadiya ya saki mahaifiyarta.

‘To ita kuma Halima ita ce babbar ‘yarta, kuma dama ta ce idan aka saki babarta to ko me ye ma zai iya faruwa da ita. Sai ta dauki wani sinadari irin na kamfanin shuka ta sha, daga bisani sai ta fito tana kukan ciwon ciki tana cewa a taimaka mata.’ in ji Kabiru Hamza.

Ya kara da cewa daga nan ne aka kai ta asibiti cikin gaggawa amma tuni rai ya yi halinsa.

Rasuwar Halimatus Sadiyya ta yi matukar tayar da hankalin iyaye da danginta, musamman ma hanyar da aka ce ta bi wajen kashe kanta.

Malama Sakina, kanwa ce ga mahaifin marigayiyar, ta kuma ce; ‘Sadiya mutuniyar kirki ce wacce ba za a manta da ita ba.’
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!