Connect with us

KASUWANCI

Za A Shekara 10 A Na Cigaba Da Fuskantar Karancin Lantarki A Nijeriya – TCN

Published

on

Ga dukkan alamu babu wata alamar ga Nijeriya wajen kawo karshen rikicin karancin da ake fuskanta.

Wannan bayanin ya na kunshe ne a cikin rahoton da kamfanin samar da wutar lantarki na kasa, TCN, ta gabatarwa da hukumar sanya ido akan samar da wutar ta kasa NERC, inda hakan ya nuna cewar, Nijeriya zata ci gaba da fuskantar karancin akan samar da wuta daga layin samar da wuta nan da shekaru goma masu zuwa.

A cewar rahoton, wannan ya faru ne saboda burin da aka sa na kirdadon samun karin matsalar na’ura da yawan samun ruwan sama da karancin samun yawan bukata karfi karanci a kasar nan zaici gaba da kasancewa a kasa akan kimanin mega watts 3,000.

A cewar rahoton, Nijeriya zata ci gaba da fuskantar kari na bukatar mega watts 15,440 da kuma mega watts 24,551 a shekarar 2027 mai zuwa.

Rahoton ya nuna cewar, binciken da hukumar kasa da kasa ta kasar Japan JICA ta gudanar ko kuma ace ta yiwa TCN ta mayar da hankali ne akan shekarar 2027 mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!