Connect with us

Uncategorized

Abubuwan Da Su Ka Biyo Bayan Kaddamar Da Majalisar Dokoki Ta Tara

Published

on

•Buhari Ya Taya Murna

•Sababbin Shugabannin Majalisar Sun Yi Alkawarin Adalci

•Ndume Ya Rungumi Kaddara

A ranar Talatar nan ne a ka rantsar da sabon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan tare da mataimakinsa, Sanata Omo-Agege bayan lashe kuri’ar da aka jefa.

Bayan rantsar da su, a cikin jawabin godiyarsa, Sanata Ahmad Lawan,  ya bayyana cewa, zai kasance mai adalci ga kowa ba tare da nuna banbanci ba.

Haka kuma, wasu daga cikin ‘yan majalisar suma sun tofa albarkacin bakinsu kan batun majalisar.

Shima a nasa sakon taya murna, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya zababbun shugabannin murna, ya kuma ba wadanda su ka fadi zaben hakuri tare da yin kira da hada kai don yin aiki tare.

Da yake jawabin na sa, Sanata Lawan ya bayyana cewa, “Zabuka sun kare yanzu. Sakamakon zaben ya nuna  majalisar majalisa ce mai hadin kai. Dukkan jam’iyun siyasa ciki har da PDP da YPP, sun zabe ni, wanda wannan ke nuna shirin majalisar na aiki tare da kuma hadin kai.”

A ci gaban jawabin sa, bayan kira ga sauran ‘yan majalisar kan bada hadin kai da jajircewa domin samun nasara da cigaba, ya kuma yi alkawarin kawo abubuwan ci gaba da za su anfani ‘yan Najeriya, mussamman ma dai talakkawa, wanda a cewar sa, su ne jigon tafiyar.

A cikin jawabin na sa har wa yau, ya tabo batu kan harkar kimiyar fasaha, inda ya ce, wannan fannin na dai daga cikin muhimman abubuwa da majalisar ta tara a karkashin sa za ta fi maida hankali.

Da ya ke bayani kuwa kan batun hulda tsakanin bangaren fadar shugaban kasa da kuma majalisar, ya bayyana cewa, za su yi aiki kafada da kafada don shawo kan matsalolin da ke addabar kasar kama daga garkuwa da mutane, barayin shanu, fadace fadace da sauran ayukkan ta’addanci.

“Za mu yi aiki tare don cimma muradan kasa.  Sannan matsalar rashin aikin yi, yawan kashe kai da gangan, cinhanci da matsalar tsaro ma, za mu yake su ba kadan ba,” in ji shi.

A fannin matsalar rashin karatun yara, wanda majalisar dunkin duniya ta lissafa kimamin yara miliyan 14 da ba sa makaranta, Sanata Lawan ya ce, za su yi aiki tukuru don shawo kan matsalar da samar da dawwamammar mafita.

Bayan kammala taron, wasu daga cikin sanatocin, sun tofa albarkacin bakinsu kan batun majalisar.  Tsohon gwamnan Kano kuma sabon zababben sanata, Malam Ibrahim Shekarau na dai daga cikin wadanda su ka tofa albarkacin bakinsu.

“Ina taya murna ga dukkan zababbun sanatoci da kuma shugaban majalisar, haka kuma, na yaba da irin halin dimokradiyar da aka nuna wurin gudanar da zaben,” in ji Shekarau

A nasa kuwa, tsohon shugaban majalisar, Adolphus Wabara cewa ya yi, sakamakon zaben alama ce da ke nuna cewar zabin ‘yan majalisar ne.

Haka kuma, ya ja hankalin sanatocin kan sauke nauyin da talakkawa su ka dora ma su, yana mai cewa, “ko dan talakkawan da su ka zabe ku, to ku yi kokari ku yi abunda ya kamata.”

Kamar sanata Mathew Urghoghide (PDP, Edo), haka shima Sanata Barau Jibrin (APC, Kano), ya yaba da yanayin da aka gudanar da zaben, yana kuma mai cewa, da irin haka, ya tabbata tsarin dimokradiya zai kara habbaka a Najeriya.

A cikin wata sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya fitar, Femi Adesina, ya bayyana cewar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya sabbin zababbun ‘yan majalisar murna .

Haka shi ma, ya yaba da irin yanda aka gudanar da zabukan ba tare da murdiya ba, inda ya kara da cewa, hakan alamar cigaban dimokradiya ne a kasar.

Shugaban kasar, wanda ya ce, majalisar jigo ce kamar yanda yake a dokar kasa, to sai dai wani abu, hadin kai tsakanin duka bangarorin  ne abunda ya kamata domin samun nasara.

Ya kara da cewa, “majalisar na da gagarumar muhimmiyar rawa da za ta bayar don cimma kudurorin gwamnati na mataki na gaba.”

Daga karshe, shugaban kasar ya yi kira ga wadanda ba su samu nasara a zaben shugabantar majalisar ba da su yi hakuri, su kuma hada hannu tare dan yin aiki gabadaya.

Bayan faduwarsa zaben, Sanata Ali Ndume (APC Borno), wanda ya kara da  Sanata Lawan, ya bayyana zaben shugaban majalisar da aka gudanar a matsayin sahihin zabe.

Ndume, wanda ya ke bayyana hakan sa’ilin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, ya ce zaben ba wai zaben a mutu ko a yi rai ba ne, a’a takara ce dai kurum.

“Yanzu zance ya kare, abokanai na (‘yan majalisa) sun zabi zabinsu, to koma dai minene, zaben sahihin zabe ne,” in ji Ndume

Sanata Ndume, wanda ya bayyana cewa haka Allah Ya kaddara, ya ce ya yarda da hakan, kuma zai dafa wa sanata Lawan dan yin aiki tare.

A sabuwar majalisar ta tara dai, Sanata Ahmad Lawan ne ya zama shugaba, inda Obie Omo-Agege ya zama mataimakin sa

A majalisar wakilai kuwa, Femi Gbajabiamila ne ya zama shugaban majalisar wakilan, inda Ahmed Wase ya zama mataimaki.

A shirin fara gudanar da majalisar dai, shugaban majalisar wakilan, Femi, ya nada Sanusi Garba Rikiji a matsayin shugaban ma’aikatansa.

Rikiji dai, shi ne tsohon shugaban majalisar jiha ta Zamfara daga shekarar 2011 zuwa 2019. Yana cikin zababbun ‘yan takarar APC da hukuncin koli ya shafa a jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!