Connect with us

LABARAI

An Bukaci Gwamnatin Bauchi Ta Saki Kudi Ga Shirin Tazarar Haihuwa

Published

on

An yi kira ga gwamnatin jihar Bauchi da ke tabbatar da sakin kudade ga bangaren shirin Tazarar Haihuwa a cikin jihar kuma a kan lokaci, domin kyautata shirin.

Jami’ar Gudanarwa na kungiyar ‘The Challenge Initiatibe’, Mrs Rabi Ekele ce ta yi bukatar a wani taron karfafa guiwar ‘yan jarida da suka shirya a Bauchi don tabbatar da ‘yan jaridan suna yin rahotonnin da suka shafi Tazarar Haihuwa a cikin al’umma, taron ya gudana ne a ofishin NUJ da ke Bauchi, hadakar kungiyar TCI da kwararrun ‘yan jaridu masu rahotonnin kan kiwon lafiya ne suka dauki nauyin shiryawa.

Rabi Ekele ta yi amanar cewar muddin gwamnatin ta sake wadattun kudaden a kan lokaci hakan ne zai baiwa ma’aikatar lafiya a jihar da hukumar lafiya tun a matakin farko ta jihar damar aiwatar da shirin Tazarar Haihuwa domin Mata da yara su samu amfanuwa.

Ta na mai bayanin cewar a shekarar 2018 gwamnatin Bauchi ta ware sama da naira miliyan 190 wa shirin Tazarar Haihuwa amma kudin an gaza fitar da shi har gwamnatin ta shude.

Ta nuna gayar farin cikinta a bisa yunkurin sabuwar gwamnatin jihar na sanya dokar ta-baci kan sha’anin lafiya, tana mai imanin cewar ta hakan shirin Tazarar Haihauwa zai samu aiwatuwa domin kyautata lafiyar uwa, iyalai da kuma Mai gida hadi da al’umma gabadaya.

Madam Rabi ta kuma fada a wajen taron cewar kungiyar tasu za su bayar da dukkanin hadin kai da goyon baya wa gwamnati domin ta sami nasarar bunkasa kiwon lafiyar jama’an jihar, da kuma samun nasara kan shirinsu na Tazarar Haihuwa.

Daga bisani ta kalubalanci mahalarta taron da su dawo da hankulansu kan fadakar da Gwamnati muhimmanci samar da yanayin da ya dace ga Shirin Tazarar Haihuwa domin a samu nasarar kyautata shirin, kana suke ilmantar da jama’a suke rungumar shirin hanu biyu-biyu.

A cewarta ‘yan jarida abokan jere ne ta fuskacin neman inganta shirin, a cewarta da bukatar manema labarun su kara ninka kokarinsu wajen yin rahotonnin kan Tazarar Haihuwa domin muhimmanci sa ga al’umma.

Madam Ekele tana mai kuma fadin cewa kungiyar ta TCI za ta ke shirya taron horaswa ga ‘yan jarida a cikin muradinsu tabbatar da ana rahotonnin kan Tazarar Haihuwa yadda ya kamata a cikin al’umma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!