Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Cafke Mai Amfani Da Sa-Hannun Jami’in Yada Labaran Gwamnatin Oyo

Published

on

Wani matashi mai suna Olabisi Johnson Fakorede, ya shiga hannun rundunar ‘yan sandar Jihar Oyo, bisa laifin yin amfani da sa-hannun babban jami’in watsa labaran gwamnatin jihar, Mista Taiwo Adisa. An dai cafke Fakorede ne a ranar Talata lokacin da ya yi amfani da sa-hannun a matsayin sakataran gwamnatin jihar. An dai samu nasarar cafke shi ne a shalkwatan karamar hukuma, inda a ka mika shi ga ofishin shugaban ma’aikatar jihar, lokacin da ya yi kokarin mallakar wani ofishi a karamar hukumar.

Babban jami’in watsa labaran gwamnatin jihar, Taiwo Adisa, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa, Fakorede ya zo cikin ma’aikatan da wasika wacce ta ke dauke da sa-hannuna, wanda ya nuna cewa na dauke shi aiki a matsayin mukaddashin sakataran karamar hukuma. Adisa ya kara da cewa, “wasikan Fakorede, ya nuna cewa, an ba shi wannan matsayin ne kamar yadda sashin na 42 (2,3) na tsarin mulkin ta shekarar 1999 ta tanada.   

“Ya bayyana wannan wasika ne tun ranar Litinin ga babbar ma’aikatar jihar, inda ya bukashi a ba shi ofishinsa da kuma motar hawa. Shugaban ma’aikatar ya bukaci ya dawo ranar Talata lokacin da kowa ya na nan. “Nan take jami’an ma’aikatan su ka tuntubi babbar jami’in watsa labaran gwamnatin jihar, inda ya tabbatar da cewa wannan wasika na bogi ce. Jami’an ma’aikatar sun hada wa mutumin tarko, inda su ka samu nasarar cafke shi a ranar Talata.

Bayan wannan kame, Fakorede ya yi akirarin cewa, ya aikata wannan laifi ne, domin ya samum aikin yi. “Lokacin da a ka tambaye shi yadda ya samu wannan wasika, sai Fakorede ya bayyana cewa, ya samu yin wannan wasika ne tun lokacin da ya fara jin sunan babbar jami’in watsa labaran a gidan rediyo. Ya kara da cewa, kullum ya na so ya samu matsayi daga wajen ‘yan siyasa.”

Fakorede ya cew, “ni dan asalin Jihar Oyo ne, amma ina zama ne a Jihar Legas. Ina yawan sauraran rediyo, kuma a nan ne na ji sunan babban jami’in watsa labaran jihar. Ina son matsayi na siyasa, wannan shi ya sa na aikata hakan. “Ni da kaina ya yi wannan wasikar, babu wanda ya saka ni”.

An gurfanar da Fakorede a wurin ‘yan sanda, domin gudanar da cikakken bincike.

Adisa ya garkade mutanan jihar da su yi hankali da masu damfara wadanda su ke amfani da sabuwar gwamnati domin damfarar al’umma.

Majiyarmu ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Mista Olugbenga Fadeyi, amma hakan ya ci tura, domin an ta kiran wayarsa amma bai daga ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!