Connect with us

LABARAI

Boko Haram: Sojojin Najeriya Sun Kubutar Da Wasu Mata Da Kananan Yara

Published

on

Dakarun Sojin Kasar nan sun ceto wasu mata biyu da kananan yara daga hannun ’yan ta’addan Boko Haram, a lokacin da suka yi wa ‘yan ta’addan kwantan bauna a kauyan Gwadala, ta Jihar Borno.

Cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da fararen hula na rundunar, Kanar Ado Isa, ya fitar, ya ce zaratan rundunar sun kasha daya daga cikin ‘yan ta’addan, sauran kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga a jikkunansu.

Ya ce, zaratan rundunar kuma sun kwato bindigar AK47 guda daya, bindigar toka guda daga hannun ‘yan ta’addan.

Kanar Isa ya ce, ìshirin yin kwantan bauna, da kakkabe sauran ‘yan ta’adda wanda Sojojin runduna ta 7 suke a kai domin taimakawa nasarorin da aka samu kawo yanzun, a farmakin, ìHalaka Dodo,î domin tabbatar da babu sauran guggubin ‘yan ta’addan na Boko Haram bisa yunkurin kawo karshen duk wata tashin-tashina da matsalar tsaro a shiyyar arewa maso gabas.

Mukaddashin Kwamandan runduna ta 7 ta Sojin Nijeriya da Kwamandan sashe na 1 na rundunar Operation Lafiya Dole, Birgediya Janar Abdulmalik Bulama Biu, ya jinjinawa kokarin dakarun Sojin na Nijeriya, sa’annan ya isar masu da gaisuwan babban hafsan dakarun kasa na kasar nan, Laftana Janar Tukur Yusufu Buratai, a kan nasarorin da suka samu kawo yanzun.

ìAna kuma bukatar al’umma da su bayar da cikakken hadin kai ga rundunar Sojin da sauran hukumomin tsaro ta hanyar ba su tabbatattun bayanai kuma akan lokaci a yakin da suke yi da ‘yan ta’addan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!