Connect with us

RIGAR 'YANCI

Kwana 44: Har Yau Babu Labarin Magajin Garin Daaura Tun Sace Shi

Published

on

Hukumomin ’yan sanda a Jihar Katsina sun ce sun yi wasu kame-kame tare da gano wasu abubuwa a kan binciken da suke yin a sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba.

A bisa lissafin wakilinmu, a yau kwanki 43 kenan da sace babban mai sarautar gargajiyan wanda wasu ‘yan bindiga suka yi a ranar 1 ga watan Mayu, a kofar gidansa da ke kan titin Daurama, cikin garin na Daura, bayan kammala Sallar Magariba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan na Jihar ta Katsina, SP Gambo Isah, wanda shi ne ya ce sun yi kamun da kuma gano wasu abubuwan, amma ya ki ya bayyana sunayen wadanda suka Kaman ko kuma abubuwan da suka gano din, ya nace da cewa, ìBa zai yiwu mu kawo hargitsi a binciken da muke yi din ba.

Sai dai ya ce, akwai kokarin da suke yi na tabbatar da Basaraken ya dawo cikin jama’arsa ba tare da ko kwarzane ya same shi ba, ya kara da cewa, suna dai kan binciken al’amarin.

Akwai kuma damuwa matuka ga iyalan Basaraken, kan faruwan lamarin, inda wasu ke cewa, wannan satar Basaraken da aka yi ta sha bamban da makamantansa da aka yi, domin an saba da zaran masu satar mutane sun saci mutum sukan hanzarta sanar da iyalansa a cikin awanni da satar na shi ko kuma kwanaki kadan.

A lokacin da aka tuntube shi ta waya, Dan Lawan Daura, Umar Umar Ata, wanda kani ne ga Basaraken da aka sace din, cewa ya yi, ba su ji wata sabuwar magana ba tun daga lokaacin da aka sace shi din.

ìMu a matsayinmu na iyalansa mun bar komai ne a hannun Allah, muna kuma ci gaba da rokon Allah Ya dawo mana da shi lafiya.

Magajin Gari, kane ne ga Sarkin Daura Faruk Umar Faruk. Wanda jami’in hukumar Kwasatn ne wanda ya yi ritaya, yana auran Hajiya Bilki, wacce ‘yar’uwa ce ga shugaba Buhari. Shi ne kuma mahaifin Fatima wacce ke auran dogarin shugaba Buhari, Kanar Mohammed Abubakar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!