Connect with us

RA'AYI

Najeriya: Allah Ya Na Son Ta Mutenen Cikinta Su Na Kin Ta

Published

on

Hakika Najeriya kasa ce da Allah ya ke son ta, amma mutanen cikinta su na ganganci da rayuwarsu na wajen kashe kasar da yi ma ta zagon kasa, wanda tarihi ya nuna tun wajen shekaru 52 da suka shige kasar nan ta shiga wasu rigingimu nayakin basasa da kashe-kashe irin na kabilanci da bangoronci, daga baya aka shiga fama da rikicin addini irinsu maitatsine da kuma rikicin Musulmi da Kirista a wasu sassan kasar nan ga baya-bayan na n rikicin boko haram dana fadace-fadacen Fulani da makiyaya ko kasha-kashe na babu gaira babu dalili, ga satar mutane domin karbar kudade koyin tsafe-tsafe, sannan wasu laifikan da suka zamo ruwan dare irinsu sace-sace da fashi da makami da fyade da  zamba da algus da zalunci da sama da fadi da kashin dankali da kama karya da cin hanci da rashawa da sonkai da rashin kishin kasa da hassada da ganin kyashi da munafurce-munafurce da hadamar mulki ko dukiya ko ta halin kaka. Yanzu banda allah yana son kasarnan, tana irin wadannan miyagun matsalolin ta ina za’a sami cigaba? Ai da tuntuni kasar nan ta wargaje kowa ya kama gabansa, ko kuma makwabtan kasar nan suyi ta tara yan gudun hijira daga kasar nan abar kasar babu kowa.

Lallai yana da kyau al’ummar kasannan kowa ya shiga taitayinsa a sa kishin kasarnan a gaba domin ciyadda ita gaba, ko ba komai akwai ‘yan baya masu tasowa, yanzu yau aka haifi wani kuma yana da hakki , tarihi kuma zai iya bayyana ace magabatansa su ne suka rusa kasarnan, saboda haka kalubale ga masu son mulki ko ta halin kaka, kuma aki tabuka abin kirki sai zalunci da wawashe dukiyar kasa.

Sannan wata shawara da zan zanbawa ‘yan siyasa masu son tsayawa takara me suka taka na son lailai sai sun tsaya takara? Kwadayin arziki ko dukiyar da ake samu cikin sauki ne yake dibarsu ko kuma domin su kece raini ko tsere sa’a ne yake dibarsu ko kuwa wata bukata ce ta kashin kansa take dibarsa ba bukatar jama’a ba? Lallai su tsaya suyi tunanai,  gadai zabe nan yana gabatowa, kasa ta fara daukar dumi, domin   dumukuradiyyar wannan kasar tamu an bawa kowa da kowa dama yazo, kaga kuwa duk abinda akace kowa da kowa to lallai dole ayi kitso da kwarkwata , dole asamu bara gurbi, saboda ganin yadda wadanda suka rike makaman siyasa suna hawa manyan motoci da gina gidaje mahadi ka ture, da yawace-yawace a duniya da tarin dukiyar da ba’a samar da ita ta kasuwanci ba, wannan ya dauki hankalin kuwa na ganin dole shima ya samu wannan dama koya kece raini, hakan tasa jaki da doki da jaba da akuya duk ido ya rufe inbakayi bani wuri, ko a mutu ko ai rai.

Wadanda damarsu bai isa su tsaya takara ba, sai ayi amfani da su wajen cin mutuncin masu mutunci a kafofin yada labarai ko a fili, a bawa wasu kayan maye suyi banga ana basu tashi ka cika naci, anya zaa sami ci gaba kuwa? Su kuma sauran talakawa masu zabe, an kwadaita musu yan kudin daba zai share  musu hawaye  na kwana uku ba, suce sunji sun gani,[ sai wane ko kofar katako] babu akida da sanin ya kamata, kudi kawai.

Inama ace wani tunani zai zowa masu kada kuri’a, duk mutumin da zasu zaba a kowane mataki, sai suyi kungiya su zauna da dan takara, su tambaye shi mai zai musu in sun zabe shi? Ko kuma su gaya musu bukatunsu dana ‘ya’yansu ayi a rubuce yasa hannu suma su sa hannu, a samu wasu lauyoyi masu kishin al’umma suma su sa hannu madadin wannan al’umma. Kaga koda yaci zai san cewa ga irin alkawarin da yayiwa al’ummarsa, domin suna iya kaishi kotu in sukaji shiru kaga wannan zai rage rashin alkawara da ake dauka ba’a cikawa.

Kuma lallai al’umma suyi wani tsari na yadda zasu koyi kiranye ga zababbun da suka zaba basu kulawa dasu, wannan shima abune mai muhimmanci amma wani abin haushi, sai kaga wasu yan tumasanci suna zaune suna karbo wani abu daga wurin ‘yan siyasa zababbu, kuma suna karesu, sunayi musu yaki a karkashin kasa, lallai ayi hankali da irin wadannan al’umma domin zomo baya fishi da makashinsa sai maratayi, hakika irin wadannan al’umma masu kare ‘yan siyasa ko shugabanni akan irin zaluncin da sukeyi, saboda suna karbar wani abu, sunfi kowa barna. Domin dasu ake rusa kasa.

Ina ma’ace ba kowane ya kamata ya tsaya takara ba sai an tabbatar da ingancinka da kishin kasa da son taimako da mutane, da ilmin shugabanci da  yana kuma da sana’a ko aikinyi bakuma azzalimi ko dan kama karya ba, lallai da anfi haka cigaba a kasar nan, hakika dukiya da matsayi sune adon wannan zamani da muke ciki, amma sai an hada da adalci, gaskiya da tsoron allah, sannan abin zaifi kwarjini sosai. Masu yakar hakan koyin zagon kasa ga masu irin wannan kyawawan halaye na cigaban kasa, tosuma a yake su kamar yadda za’a yaki ‘yan tada zaune tsaye, koda hukuma takauda kai akansu, to al’umma su dauki nauyin yakin dasu ta fuskar kyama da janye jiki dasu.

Saboda haka zaben kato bayan kato shine zai magance duk wata matsala a wajen fidda ‘yan takara, in ma haka za’ayi a zaben gama gari? to amma fa kar a manta dan Nigeria yana da tunanin daya kware a wajen lalata tsari, saboda in ba’ayi hankali ba, nan ma za’a iya fito da wasu hanyoyi da zasu yiwa tsarin zagon kasa, har ace gwara zaben (delegate). saboda haka sai ansa ido sosai da sosai. A bangaren hukumar zabe kuwa kada ta kasa yin tsarin daya kamata har yakai ga lalacewar tsarin, musamman rashin kayan aiki jami’an tsaro ko bata lokaci.

Shikuma shugaban kasa muhammad buhari mai gayya mai aiki, babban aikin dayake gabansa da zai taimakawa talakawa masu zabe, shine yayi kokari ya taimaka wajen nunawa talakawa mutanen da yake ganin lallai abokan aiki ne irinsa, ma’ana suna kamanta gaskiya da rikon amana da biyayya a shugabancinsu, da bada shawarar lallai a sake zabarsu su dawo, wadanda suke bata tsari ko ‘yan son zuciya suma ya fito karara yayiwa talakawa masu zabe bayaninsu daya bayan daya, da irin matsalar da suke haddasa wajen hana shugabancinsa armashi kuma ya gayawa al’umma kada a sake zabarsu tun daga kan gwamnoni zuwa ‘yan majalisar tarayya da wakilai data dattijai haka gwamnoni ma su fito suyiwa al’umma bayanin irin mutane da za’a zaba masu kishin kasa da hanawa a zabi wadanda basu tabuka komai ba, sai yaudara da hana kawo cigaba. Indai za’ayi wannan gaskiya da gaskiya to shugaban kasa ya fita ko ba sabulu. Amma in yayi shuru da nufin wai demokoradiyya tayi aikin kanta to gaskiya za’a koma gidan jiya wannan shine bashin da talakawa suke bin shugaban kasa, domin kowa yasan babu wanda yafi shugaban kasa samun rahotannin dukwani jami’in gwamnati  dama duk wasu al’umma (security report), saboda haka zai san duk irin wainar da ake toyawa a kasa baki daya, haka gwamnoni, lallai in har za’ayi wa talakawa irin wannan gatan za’a taimaka masu susan mutanen kirki masu san kawo cigaban su da masu  hana musu cigaba. Domin talaka mai zabe makaho ne baya rarrabewa da barcin makaho, ana dai yi masa kwarjini da dadin baki, kwalliya, mota mai tsada, gida nagani na fada, a kuma a watsa masa ‘yar tsaba, yayi gaba, ba tare da sanin irin illar da ake yi masaba. Kuma hakan zai magance matsalar na ta kaci bakaci ba kaci.

Gadai dama nan, an gama saida form din masu tsayawa takara har an gama zaben kato bayan kato ayi amfani da wannan damar a tace, har wadanda sukai tsalle suka koma wasu jam’iyyun, ai wani wayo ne anan in mutum bashi da cancanta na sake tsayawa zabe, saboda rashin gaskiya, a dawo masa da kudin form dinsa da nufin allah ya raka taki gona, in kuma yayi rawar gani a tsai dashi ya koma, haka sabbin ‘yan takara a kula da kyau sai yana da wasu halaye da zai kamanta kuma mai sana’a da ilmi da ake bukata.baka da sana a ka shiga siyasa,lallai akwai alamar tambaya.  Kuma  a sa sanda a kore siyasar ubangida data kudi a Nigeria, wannan ma zai taimaka a daina cushe ko kitso da kwarkwata. Kuma wani abin mamaki sai kayi tambaya ina sarakunan gargajiya da malaman addinai da masu hali da masu fadi aji da yanboko,mai zai sa bazasu tsaya kai da fata su tace duk wasu ’yan takara tun daga kowanne kananan hukumomin kasarnan a tabbatar da cancanta da nagarta,amma a cire  son zuciya,kuma ayi hakan tun daga zaben kansula zuwa na shugaban kasa,shi kuma talaka ya yarda ya zabi abin da shugabanninsa sukai amannar shine mafita ,hakan zai haifar da kishin kasa da hadin kai da son juna a zukatan yan kasa.

A karsheina dab da rufe wannan batu, sai ga wani abu na daukar hankali, wanda ake nunawa a kafofin sadarwa na zamani wato (social media) wacce wata jarida mai suna (daily nigerian) tace ta gano, to abinda ‘yan majalisar jahar kano sukayi sunyi daidai, amma yanada kyau a bawa jam’iyar APC ta kasa dama tainata bunciken, akuma bawa hukumar EFCC da fadar shugaban kasa da manyan kungiyoyi masu zaman kansu da masana dama suma suyi nasu bunkicen, domin tabbatar da adalci. Shikuma mai girma gwamna yayi addu’ar Allah yasaka masa in har wannan abu sharri ne.watakila ya zamar masa wata muhimmiyar daukaka.

Daga Abdullahi Idris Yakasai

Email addres: [email protected]

Gsm No: 08054407095
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!