Connect with us

RIGAR 'YANCI

Rashin Halartar Alkali Ya Kawo Tsaiko A Shari’ar Maryam Sanda

Published

on

Rashin zuwan alkali ya kawo tsaiko a kan shari’ar kisan kai da ake yi wa Maryam Sanda, ya tsayar da ci gaban shari’ar.

Ana yi wa Maryam shari’a ne a gaban babbar kotun da ke zama a Maitama, Abuja, a bisa zargin da ake yi mata da kashe mijinta mai suna, Bello, wanda dan’uwa ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Bello Haliru Mohammed, a shekarar 2017.

Ana tsare da ita ne tare da dan’uwanta, Aliyu Sanda, mahaifiyarta, Maimuna Aliyu da mai yi masu hidima a cikin gida, Sadiya Aminu, wacce ake tuhuma da taimakawa wajen lalata duk wata shaida ta jinin daga wajen da aka aikata laifin.

Sai dai kotun ta amshi bukatar da Lauyan da yake kare sauran mutanan uku, ta sallame su a kan laifin da ‘yan sanda suke tuhumar su da aikatawa.

Alkalin da yake shari’ar, Mai Shari’a Halilu Yusuf, ya sanya ranar 6 ga watan Mayu a matsayin ranar da wanda ake tuhuma za ta fara kare kanta, bayan da ya ki amincewa da bukatar cewa ba ta da wata tuhumar da za ta amsa  da Lauyanta ya shigar a madadin ta. Amma a ranar 6 ga watan na Mayu sai aka shaidawa masu cewa Mai Shari’a Yusuf yana wajen kotun musamman mai shari’ar kararrakin zabe ta Jihar Ogun, sai aka cimma matsaya a kan ci gaba da shari’ar a ranar 11 ga watan Yuni, domin ci gaba da shari’ar.

Sai dai shari’ar ta sake samun tsaiko a jiya din, domin an sake shaida masu cewa, har yanzun mai shari’ar yana can jihar ta Ogun.

Wani jami’in kotun ya shaidawa wakilinmu cewa an sake sanya ranar 10 ga watan Satumba domin ci gaba da shari’ar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!