Connect with us

LABARAI

Sabuwar Ranar Dimukradiyya: Za Mu Fara Fallasa Masu Aikata Cin Hanci Da Karban Rashawa – Buhari

Published

on

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sabuwar dabarar gwamnatinsa ta yakar cin hanci da karban rashawa a kasar, ya na mai cewa, duk wadanda su ke aikata cin hanci da karbar rashawa za mu yayata sunayensu mu kuma ba su kunya. A lokacin da yake jawabi wajen taron lacca a kan ranar Dimokuradiyya a Abuja, ya ce, gwamnatin na shi za ta rungumi alíadar shelantawa duniya da kuma kunyatar da duk masu karban cin hanci da rashawa za kuma ta karrama wadanda ba sa aikata hakan.

Ya ce, a yanzun haka, gwamnatin na shi tana kan kididdigar nasarorin da ta samu ne ta fuskacin yakar cin hancin da rashawa, tana kuma dubawa ta ga abin da ta yi da kuma wuraren da take da bukatar yin gyara a kansu gami kuma da irin sabbin dubarun da ya kamata ta bullo da su wajen kalubalantar wannan matsalar. ìIna farin cikin sanar da ku cewa, har ma mun fara bin wannan hanyar a bisa tattaunawar kwanan nan da kwamitin yakar cin hanci da rashawa ya yi da dukkanin hukumomin da suke yin aiki a wannan bangaren.

Shugaban kasan ya ce, gwamnatin na shi za ta toshe dukkanin kafofin da ake samun sabani a tsakaninta da majalisa domin ta samar da cikakken hadin kai da sashen shariía. Ya ce, za kuma su karfafa dokar nan ta tilastawa manyan jamiían gwamnati bayyana kadarorin da suka mallaka, su kuma sanya takunkumi mai karfi a kan Lauyoyi, Bankuna, masu hannayen jari, manyan jamiían gwamnati da sauran daidaikun mutane da suke taimakawa masu aikata cin hanci da karban rashawa.

Shugaban kasan ya yi jimamin yanda harkokin siyasan da aka kammala a kwanan nan shaíanin amfani da kudi ya dabaibaye su. irin hakan yakan haifar da mummunan abu ne a cikin kasa, tafuskacin baiwa masu zabe ëyancin zabar abin da suke so, ta yanda suke daukaka mutanan banza zuwa ga mukaman shugabancin da ba su cancance su ba, su kuma lalata maíanar mulkin dimokuradiyya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!