Connect with us

Uncategorized

Ta Kashe Kanta Saboda Mahaifinta Ya Saki Mahaifiyarta A Kano

Published

on

Wata budurwa mai shekaru 17 da haihuwa, mai suna, Sadiya Shehu, da ke zaune a Anguwar Tudun Murtala, ta karamar hukumar Nasarawa, Kano, ta kashe kanta a ranar Litinin, sabili da sabanin da ya shiga tsakanin mahaifanta wanda har ya kai ga mahaifinta ya saki mahaifiyarta. Ta mutu ne a dalilin kwankwadar maganin kashe kwari wanda aka fi kira da fiya-fiya da ta yi a dakin mahaifiyar nata. A lokacin da wakilinmu ya isa gidan da abin ya faru, ya iske mutane suna ta tururuwa domin yi wa iyalan gidan taíaziyya.

Da yake zantawa da wakilin namu, mahaifin mamaciyar, Malam Shehu A Lawan, ya tabbatar da mutuwar Sadiya din ta hanyar kashe kanta da ta yi, ìsaboda dan karamin abu da ya faru,î a tsakanin shi da mahaifiyarta a ranar Lahadi, wanda kuma aka sasanta shi tun a wannan ranar.

ìNa dan sami matsala da mahaifiyarta a kan wani abu, wanda hakan bai yi mata dadi ba. Ta yi ta kuka, na kuma shaida mata shi kenan babu komai, komai ya wuce. Na fita tun da safe na bar Sadiya da kannenta cikin koshin lafiya, amma abin takaici, ina wajen aiki sai aka kira ni a waya cewa an kai ta Asibiti. Likitoci sun yi bakin kokarin su domin su ceto ranta, amma kaddarar Allah ta riga fata, sai ta mutu, in ji Malam Shehu.

Da aka tambaye shi ko an yi wa Sadiya baiko da wani kafin mutuwar nata. Lawal ya tabbatar da cewa Sadiya tana da saurayi wanda yake neman ta da aure, ìA baya-bayan nan da na y i magana ma da saurayin nata, ya tabbatar mani da cewa zai turo iyayensa domin su zo mu zauna da su a kammala maganar auren na su da zaran mahaifinsa ya dawo daga aikin Umrah da ya tafi a kasar Saudiyya. Amma ashe Allah Ya kaddarta wannan auren ba za a yi shi ba, domin  a amaryar nan ta mutu. Ina kaunar marigayiya Mama (Sadiya) fiye da dukkanin sauran ëyaíyana. A matsayina na Musulmi na karbi wannan kaddarar, ina kuma rokon Allah Ya jikanta da rahamarsa,î in ji shi.

Mahaifiyar Sadiya, Malama Amina Shehu, cewa ta yi rikicin ya fara ne a lokacin da wata mai suna Maryam, wacce ëyaríuwan mijin nata ne, ta zo tana dukan dan karamin kanin mamaciyar sai shi ma mijin nata ya yanke shawarar horon yaron shi ma. ìMaryam ta zo ta fara fada da yaron nawa, Daddy, cewa ya zage ta. Da babanta ya fito daga wajen wanka, sai ya fara dukansa kamar zai kashe shi, sai na kasa daurewa, sai na ce masa dukan fa ya wuce iyaka ko da kuwa ya aikata abin da take zargin na shi da aikatawa. Sai mijin nawa ya ce na kyale shi ba ruwana, na ce ma shi ba zan kyale ba, domin babu wanda ya zo domin ceton yaron. Mijina ya ce na yi shiru da baki na, na ce ma shi ba zan yi shiru ba tunda ba mai ceton yaron. Na ce ma shi in ma har ya zage ta wa ya koya ma shi zagin, ba abin da ya ji ana yi ba kenan a cikin gidan ba kenan?

Amina ta kara da bayanin cewa, sai mijin nata ya fusata har ya furta cewa ya sake ta a gaban mamaciyar. ìCewa ya yi na bar ma shi gida ya sake ni, sai mamaciyar ta durkusa tana ta rokonsa cewa kar ya bari na bar gidan, saboda in na bar gidan za su shiga matsala sosai,î in ji ta. A washegari ne bayan na kwashe kayana daga gidan, sai na fahimci irin bacin ran da mamaciyar take a cikinsa. Na ce mata inda a dalilin an sake ni ne kar ta damu domin komai ya wuce a wurina. Amma abin takaici, sai ta shiga cikin daki ta kwankwadi maganin kwari ta mutu. An dai yi janaíizar Sadiya a ranar Litinin kamar yanda Addinin Musulunci ya tanada. Kakakin rundunar ëyan sanda na Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, ya ce ëyan sanda ba su karbi wani rahoto a kan hakan ba tukunna, amma ya yi alkawarin nemo bahasin abin da ya auku din daga babban jamiíin ëyan sanda na yankin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: