Connect with us

Uncategorized

Wani Mashayin Direba Ya Murkushe Mutane Da Dama A Legas

Published

on

Wani direban kamfanin fiyowata mai suna Ademola Awe, ya murkushe mutane da dama har lahira a kan hanyar Ekundayo da ke karamar hukumar Epe ta Jihar Legas. Wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da Esther Orimisan ‘yar 24, Kofoworola Orimisan dan shekara 17,  Emmanuel Orimisan dan shekara biyu da haihuwa da kuma wani dan acaba mai suna Femi Shojedo.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, Awe ya na tuka motar fiyowata mai lamba kamar haka GGE 42 DN, lamarin ya afku ne ranar Asabar da misalin karfe 11 na dare, inda direban ya yi tatul da giya  kafin ya fara tuki, ya bugi wata mota a kan hanyar, inda ya yi kokarin gudu.

Wani wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa mai suna Bode Abisoye, ya bayyana cewa, wadanda lamarin ya rutsa da su ba su san cewa motar ta na zuwa ba a wannan hanya. Ya kara da cewa, direban motar mai suna Awe ya kashe fitillar motar. Ya ce, Awe ya yi kokarin gudu daga wajen da lamarin ya faru, amma sai mazauna yankin su ka cafke shi.

Abisoye ya ce, “Awe ya na tuka motar ruwa ne, ya dai yi kokarin gudu, amma saboda ya na cikin maye sai a ka damke shi, ya dai kashe wutar motar ne a kan hanyar Ekundayo, wannan ne ya janyo ya sa ya murkushe dan acaba tare da fasinjojinsa guda uku, wanda dan acabar ya dauko a kusa da asibitin ‘Modal Hospital’. Mun fada masa ya tsaya ya ceci wanda lamarin ya rutsa da su, amma ya ki.

“Mun samu nasarar damke shi, lokacin da mu ka matso kusa da shi, sai mu ka ji ya na warin giya. Mun yi kokarin kunna wutar motar, idan ba dan an samu taimakon ‘yan sanda tare da wasu jami’an tsaro daga makwabtar yankin, da direban ya gudu. “Bayan dan acabar,fasinjoji guda 3 wanda su ka hada da mata guda biyu da kuma yaro dan shekara biyu sun jikkata. Dukkan wadanda lamarin ya rutsa da su, su na raye lokacin da lamarin ya faru, amma daga baya sun mutu a babban asibitin Epe sakamakon mummunar raunika da su ka samu a jikinsu.”

Wani dan uwan yada daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su mai suna Ayo, ya bayyana cewa, ya na kan hanyarsa ta zuwa gida lokacin da lamarin ya afku. Ya kara da cewa, mahaifiyarsa ce ta bayyana masa faruwar lamarin. Ya ce, “duk dare dan acaban ya na kai su gida, a ranar lamarin ya faru, ya dauko su daga shagon mahaifiyarsu wanda ya ke kan titin Omojole.  Dan acaban ya na kan titin Ekundayo lokacin da motar ta murkushe su. Sun kusa da gidansu da ke kan titin Mosalasi lokacin da hatsarin ya faru.   

“Ina mamaki yadda Awe ya ke tuki cikin dare ba tare da ya kunna fitilla ba, idan da ya kunna wutar motar, da dan acaban ya ga motar, sannan da lamarin bai faru ba. Direban ya na tuka motar kamfanin fiyowata daga abinda na ji, an damke shi, sannan an kai shi ofishin ‘yan sanda da ke Epe.”

Lokacin da a ka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Bala Elkana ya bayyana cewa, wani mutum mai suna Shakiru Ajayi ya kai rahotun lamarin ga ‘yan sanda. Ya kara da cewa, an damke Awe, sannan an ijeye gawarwakin wadanda lamarin ya faru a dakin ijiye gawarwaki da ke babban asibitin Epe domin yi gwaji.

Elkana ya ce, “a ranar Asabar 6 ga watan Yunin shakarar 2019, da misalin karfe 11.30, wani mutum mai suna Shakiru Ajayi ya kai wa ‘yan sanda rahoton cewa, mota ta murkushe wani dan acaba a kan titin Ekundayo da ke Epa. Hatsarin ya rutsa da mota mai lamba kamar haka GGE 42 DN, wanda Ademola Awe ya ke tukawa, inda ya murkushe babur kirar Bajaj mai lamba kamar haka LSR 99 OG, wanda wani mutum mai suna Femi Shojedo ya ke tukawa.

“Dan acaban ya dauko iyalai guda uku, kuma dukkan su sun samu mummunar raunika, inda a ka garzaya da su zuwa babban asibitin Epe domin yin jinya, daga baya Shojedo tare da Esther Orimisan ‘yar shekara 24, Kofoworola Orimisan dan shekara 17 da kuma Emmanuel Orimisan mai shekaru biyu, duka sun mutu. An ijiye gawarwakinsu a asibiti domin yin gwaji. A halin yanzu direban ya na hannunmu.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!