Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basarake A Sabon Farmaki A Katsina

Published

on

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken garin Labo da ke cikin karamar hukumar Batsari ta Jihar Katsina, a ranar Talata da rana. Ba a bayyana sunan basaraken ba, an yi garkuwa da shi ne da misalin karfe daya na rana a gonarsa tare da wasu mutanan kauyen.

Wata majiya ta bayyana cewa, ‘yan bindigar sun mamaye gonar da babura, inda su ka dunga harbe-harbe ba tare da lakari ba. lamarin ya jawo tashin hankali inda su ka yi garkuwa da basaraken garin., yayin da wadanda su ke tare da shi su ka gudu.

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Laraba. Ya bayyana cewa, “wannan labarin gaskiya ne. A halin yanzu ana kokarin yadda za a ceto basaraken daga hannun wadanda su ka yi garkuwa da shi. ‘Yan sanda sun samu kiran waya a lokacin, amma da gonarsa ya na da nisa da dajin Rugu, kafin ‘yan sanda su isa wurin, ‘yan bindigar sun gudu zuwa cikin dajin Rugu. Mu na bukatar taimako ta yadda za mu ceci wanda su ka yi garkuwa da shi.“Rundunar ‘yan sanda ta na kiran mutanan yankin da su dunga zuwa gona cikin tawaga tare da sanar wa jami’an tsaro duk motsin da ba su gane ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: