Connect with us

Uncategorized

’Yan Sanda Sun Ceci Wani Barawo Daga Hunnun Mutane A Akwa Ibom

Published

on

A cikin wannan makon ne, rundunar ‘yan sandar Jihar Akwa Ibom ta ceto wani saurayi mai shekaru 18, wanda a ke zargin barayo ne daga hannun wasu fusatattun matasa. An cafke wanda a ke zargin ne lokacin da ya saci kayan sawa a shago mai lamba 18 da ke kan titin Ukua cikin garin Eket.

Wani waanda lamarin ya faru a gaban idanunsa mai suna Mista Solomon Akpan ya bayyana cewa, wanda a ke zargin dan asalin garin Ikot Ekpene, an samu nasarar cafke shi ne lokacin da ya tattara kayan sawa a wani shago cikin dare. A cewar Solomon, “lokacin da mai shagon Affiong ta zo shagon da safe, ta tarar da barawon kwance a kasa ya kasa gudu. Lokacin da a ka tuntubi Affiong, ta bayyana cewa, ta ji tsaro lokacin da ta bude shago sai ta samu wasu kayayyaki a kasa. “Na tsorata lokacin da na bude shago na samu wani mutum a ciki, inda na yi ihu makwabta su ka cafke shi.”

Mai shagon Mista Tommy Edoho, ya bayyana cewa, bayan da a ka yi wa wanda a ke zargin bugun kawo wuka, sai a ka mika shi ga shugaban matasan kauyen Ekpene Ukpa, Mista Ime wanda a ke yi wa lakabi da ‘Presido’domin gudanar da bincike.

An bayyana cewa, fusatattun matasa daga kauyen Ekpene Ukpa, sun cigaba dukan wanda a ke zargi a kusa da cocin Later Glory Church, inda su ka nemi su kone shi. Sun ta kiran barayo a kashe shi, wasu sun yi kokarin kawo fetur su kone shi.

Shugaban matasan Mista Ime ya kasa shawo kan matasan, inda ya kira ‘yan sanda daga Eket su ka cece shi daga hunnun matasan.

Da a ke ganawa da shi ta wayar salula, kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Supol Odikko Macdon ya bayyana cewa, ba a kai lamarin zuwa shalkwatan ‘yan sand aba, amma ya tabbatar da cewa, za a gudanar da bincike, sannan a gurfanar da masu laifi a gaban kuliya. Ya umurci ‘yan sandar Eket su mika lamarin zuwa kotu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!