Connect with us

KASASHEN WAJE

’Yan Tawayen Janjaweed Sun Kashe Mutane 9 A Darfour

Published

on

Kungiyar yan tawayen Darfur da ake kira Janjaweed ta kashe mazauna wani kauye su 9 a yankin Darfur.Kwamitin likitocin dake shirya zanga zanga a kasar yace an kashe mutanen ne a ranar litinin da ta gabata, a kauyen Al Dalij dake Tsakiyar Darfur.

Hukumomin Sudan sun sanya yayan kungiyar Janjaweed da tayi kaurin suna wajen cin zarafin Bil Adama cikin rundunar dake taimakawa jami’an tsaro a Yankin.

A baya dai Dakarun Majalisar Dinkin Dinkin Duniya dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur dake kasar ta Sudan sun bayyana damuwar su kan sabon tashin hankalin da aka samu tsakanin kungiyoyi da masu ruwa da tsaki a harakar tsaron kasar ta Sudan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: