Connect with us

LABARAI

Zan Tsamar Da Mutum Miliyan 100 Daga Talauci A Shekara 10 – Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci zuwa ga tudun mun tsira a cikin shekaru 10 ma su zuwa.

Shugaban kasar ya yi wannan alkawarin ne a wurin bukin ranar dimokradiya da aka gudanar ranar Laraba a Abuja.

Buharin ya kara da cewa, gwamnatin sa za ta yi kokari wurin tabbatar da kawo cigaba a tattalin arzikin kasa da zai fitar da ‘yan Najeriya daga talauci.

“A na hasashen nunkuwar   arzikin kasa (wato abunda ake kira GDP) da kaso 2.7 a wannan shekarar.

“Asusun kudin shigar gwamnati ya karu da kudi dala biliyan 45, wanda wannan kadai ya isa ya yi mana ayukka na tsawon wata tara,” in ji Buhari a cikin jawabin nasa.

A bayanin sa, gwmnatinsa ta dora ginin tubalin daukar ingantattun matakai don kawo ci gaba a kasar da tsamar da mutane daga kangin talauci da su ke ciki

“A matakin farko, za mu fara da daidaita tattalin arzikin mutanen karkara da na kasa ta hanyar bayar da kayayyakin aikin noma da kuma bayar da bashi ga mutanen karkarar, tare da samar da ingantattun hanyoyi domin zirga-zirga.”

“Na biyu kuwa, za a taimaka wa da kananan ‘yan kasuwa ta yanda za mu taimaki harkar kasuwancin gida domin cigaban kasarmu.”

Buharin ya bayyana cewa, a shekara hudu na mulkin sa da zai gabatar yanzu, zai mayar da hankali wurin inganta rayuwar al’ummma tare da daukar matakai don magance matsalolin da ke addabar kasar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!