Connect with us

SIYASA

Akwai Rawar Da Mata Za Su Taka A Fannin Yada Labarai – Ronald

Published

on

Shugaban bangaren watsa labaran na majalisar Dinkin Duniyar Mista Ronald Kayanja shi ya bayyana hakan a wajen taron kimiyar watsa labarai ta 2019, da majalisar Dinkin Duniya ta shirya a jihar Legas.

Masalisar Dinkin Duniya ta bukaci ‘yan mata su ringumi kimiyar watsa labarai. Saboda mahimmancin wanan aiki , a wanin lokacin dole sai anyi amfani da mata wajen aikin kimiyar yada labarai.

Shugaban jami’in yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya dake aiki a Nijeriya Mista  Ronald yace; cibiyarsa tana shirya bangarorin da za’a rika koyar da yan mata harkokin yada labarai na zamani.

Ya ce;  cibiyar yada labarai ta Majalisar Dinkin Duniya tana kara fadada hanyoyin koyon sana’o’i  ga alumma masamman mata kanana masu tasowa.

Mista Ronald Kayanja da yake jawabi a bikin tunawa da mahimmancin harkan yada labarai na shekarar 2019 yace; akwai hanyoyi da dama cikin aikin jarida da ya kamata ace mata sun bada gudumawa a wanan fannin.

Yace; mata dake aikin yada labarai suna wakiltan Shugabanni wajen kara fadakar da mata hakokin da yarataya a wuyansu game da iyalansu.

Sanan suna wayar dakan mata masamman mazauna karkara . Majalisar Dinkin Duniya tana alfahari da rawar da mata masu aikin sadarwa keyi.

Ya ce; za mu ci gaba da janyo hankalinsu da nuna masu yadda za su rika gudanar da ayyukan cigaba harkokin sadarwa  domin mahimmancin mata a wanan fsnnin .

Itama da take jawabi a madadin  mata na kungiyar tarayyar Afirika Madam Comfort Lamprey tace ; wanan hanyar da cibiyar yada  Labarai na Majalisar Dinkin Duniya ta kirkiro domin  mata ba karamin nasara bane.

Saboda zai taimakawa mata a fannonin sana’o’i da kuma ilimintarwa da wayar da kan mata da yara.

Ta ce ; suna jin adadin yadda Majalisar Dinkin Duniya take kirkiran hanyoyin sana’a saboda bunkasa rayuwar mata marasa galihu dama masu rayuwa a sansanin gudun hijira.

Ta kara da cewa ana koyar dasu harkokin kasuwanci da kananan sana’o’i , dama hanyoyin ci gaba yadda za su amfani rayuwarsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!