Connect with us

SIYASA

Talauci Ke Kawo Yawan Tashin Hankali A Nijeriya –Buhari

Published

on

Shugaban  Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce akwai alaka tsakanin talauci da tashe-tashen hankulan da ake fama da su a kasar nan.

“Idan bambanci tsakanin masu kudi da talakawa ya karu, to sai rashin zaman lafiya ma ya karu, “ a cewar shugaban, wanda ke magana a ranar bikin cika shekara 20 da kawo karshen mulkin soji a kasar.

Ya kara da cewa: “za mu ta iya fitar da mutum miliyan 100 daga talauci cikin shekara 10 idan aka samu kyakkyawan shugabanci da sanin ya kamata”.

Shugaba Buhari, wanda ya fara wa’adi na biyu a karshen watan Mayu, an zabe shi ne bisa alkawarin samar da zaman lafiya da yaki da cin hanci da rashawa.

Sai dai yayin da aka samu raguwar hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa, an kuma samu karuwar sace-sacen jama’a da hare-haren ‘yan bindiga a wasu sassan kasar.

Shugaban ya kuma ce tun da kasashen China da India da Indonesia suka ci gaba, to babu abin da zai hana Najeriya cigaba.

Sai dai bai yi wani cikakken bayani kan yadda zai yi hakan ba, abin da ya sa masanin tattalin arziki Abubakar Aliyu ya ce zance ne kawai.

“A yanzu babu wani tsari a kasa da ake da shi da zai nuna cewa hakan mai yiwuwa ne, a don haka ina ganin kalamai ne kawai irin na ‘yan siyasa da sukan yi,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

Najeriya ta fi kowacce kasa yawan arzikin man fetur da kuma jama’a a Afirka, amma tana sahun gaba-gaba a jerin kasashen da ke fama da rashin ci gaba, abin da ake alakantawa da cin hanci da rashin ingantaccen shugabanci.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: