Connect with us

LABARAI

Nijeriya Ce Ta 16 A Kasashen Da Ke Fama Da Rikice-Rikice

Published

on

Wani rahoton bincike ya bayyana Nijeriya a matsayin kasa ta 16 da ke kan gaba wajen fama da tashe-tashen hankula a duniya, abin da ke nuna cewa, Nijeriyar ta ci gaba da rike matsayinta na bara. Rahoton ya nuna cewa har yanzu kasashen Iceland da New Zealand ne ke kan gaba wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, yayin da kasar Portugal ke a matsayi na uku bayan ta hau kan kasar Austria wadda ta haye matsayi na uku a bara.

Yanzu haka kasar Siriya ce ke a matsayi na biyu wajen fama da rikice-rikice, inda aka bayyana Afghanistan a matsayi na farko wajen samun tashe-tashen hankula a duniya. Rahoton wanda Cibiyar Tattalin Arziki da Kididdigar Zaman Lafiya ta Ukraine ke fitarwa duk shekara, ya ce, kasashen Sudan da Masar da Arewacin Marcedonia da Rwanda sun samu gagarumin ci gaba wajen samun kwanciyar hankali a bana.

Haka zalika a wannan karon rahoton ya ce, an samu raguwar mutanen da ke rasa rayukansu a sakamakon rikice-rikice musamman a kasashen Siriya da Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: