Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Mubeena’

Published

on

Suna: Mubeena

Tsara Labari: Fauziyya D. Sulaiman

Kamfani: Maishadda Investment

Shiryawa: Abubakar Bashir Maishadda

Umarni: Ali Gumzak

Jarumai: Ali Nuhu, Jamila Umar Nagudu, Nuhu Abdullahi, Hauwa Waraka, Abba Elmustafa, Masa’uda Ibrahim, Ladidi Fagge, Maryam CTB, Hamza Indabawa, Baba Hasin da sauransu.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Adnan (Ali Nuhu) ya fito daga falo tsakar dare yana waya da budurwar sa gami da nuna mata cewar ta daina kiran sa a irin wannan lokacin, a wannan ne matar sa Mubeena (Jamila Umar Nagudu) ta fito daga daki tana tuhumar sa da laifin cin  amanar ta wajen yin mu’amula da matan banza, nan fa Adnan ya fada mata gaskiyar magana akan wadda zai aura. Jin cewar Adnan zai kara aure ne hakan ya tashi hankalin Mubeena ta soma rokon sa akan ya janye maganar auren sa, yayin da shi kuma ya kafe akan kudirin sa na son kara aure.

Ganin damuwar da Mubeena ta shiga ne hakan ya soma damun Adnan saboda yana son matar tasa, amma sai abokin sa (Abba Elmustafa) ya karfafa masa guiwa wajen ganin ya kara auren. Ita kuwa Mubeena sai ta kwarzabi kanta ta shiga matsananciyar damuwa gami  da cigaba da rokon Adnan akan ya janye maganar auren sa amma sai ya nuna hakan ba  abu ne da zai yiwu ba. Ganin cewa Mubeena batayi galaba akan mijin ta bane sai ta fara tsiro masa da mugayen halaye gami da neman lallai sai ya saketa, amma Adnan ya nuna sam bazai rabu da ita ba.

Ganin miyagun halayen da Mubeena ta tsiro da su ne hakan yasa Adnan yakai karar ta wajen mahaifiyar ta (Ladidi Fagge)  don aja mata kunne, amma hakan ma bai sa Mubeena ta daina neman hanyar da zata ruguza auren nasa ba. Kwatsam wata rana Maimuna (Hauwa Waraka) kawar Mubeena ta ziyarce ta kuma ta samu labarin halin da take ciki, jin haka ne yasa Maimuna ta bata wata gurguwar shawara, wadda kuma Mubeena tayi amfani da shawarar wajen zuwa gidan iyayen Halima (Masa’uda Ibrahim) wato budurwar Adnan wadda zai aura. Mubeena taje ta samu Halima a lokacin da take hira da Adnan a kofar gida ta ja ta da rigima har suka kaure da dambe wanda sai dakyar Adnan ya raba rigimar ya tura Halima cikin gida.

A sannan ne kuma Adnan ya nuna wa Mubeena bacin ran sa sosai, wanda hakan yasa tayi yaji ta koma gidan su, saidai kuma daga baya kawar ta Maimuna ta zuga ta suka sauya salo ta hanyar yiwa Adnan kazafin cewa yana dauke da cutar kanjamau, dalilin hakan ne yasa Halima ta dage akan sai sun je an yi musu gwaji sannan zata aure sa, haka suka je duk aka gwada su kuma aka tabbatar da ba sa dauke da cutar. Yayin da a karshe kuma Adnan yasa jami’an tsaro suka kama Maimuna saboda gane cewar da sa hannun ta a cikin makircin da Mubeeena ta kulla masa. Haka dai aka yi auren sa da Halima, sai dai kuma tun a ranar bikin dinner Mubeena ta kulle Adnan a bandaki wanda hakan yasa bai samu damar halartar taron ba, dalilin hakan ne kuma ya tashi hankalin Halima har hakan ya zamo sanadin kwanciyar ta a asibiti. Sai dai kuma a  ranar da Halima ta tare a gidan Adnan Mubeena ta tubure akan sai ya saketa. Haka kuwa Adnan ya saketa ta koma gidan su ta soma rayuwa cikin kunci da talauci domin iyayen ta basu goyi da bayan muguwar halayyar ta ba.

Ita kuwa Halima tun bayan auren ta ne sai tsohon saurayin ta Nasir (Nuhu Abdullahi) wanda ya kasance rikakken dan shaye shaye yazo kofar gidan mijin ta yana yi mata tabbaci akan barazanar bazai bari ta zauna lafiya da mijin ta ba tunda shi bata aure shi ba.

Ita kuwa Mubeena sai hankalin ta ya tashi a lokacin da ta samu labarin ‘ya’yan ta basa samun cikakkiyar kulawa daga wajen Halima. Hakan yasa tayi nadamar abubuwan da ta aikata sannan ta soma bin hanyoyin neman gafarar Adnan don ta koma gidan sa. Cikin dan lokaci kadan Adnan ya mayar da Mubeena dakin ta gami da yi musu nasihar zaman lafiya tsakanin ta da kishiyar ta Halima.

Abubuwan Birgewa:

1- Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa, haka kuma anyi anfani da kwarewa wajen rike me kallo har zuwa inda ake son a nusar dashi.

2- Camera ta fita radau, haka ma sauti ba laifi.

3- Jaruman sun yi kokari wajen taka rawar da ta daje.

4- Daraktan yayi kokari wajen ganin labarin ya tafi yadda ya dace.

5- Anyi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin.

Kurakurai:

1- Sunan fim din wato “Mubeena” ba kalmar Hausa bace, bai dace a rubuta sunan a haka ba, mafi kyawu shine a rubuta shi a Hausance wato “Mubina” domin an nuna cewa fim din bahaushen labari ne mai wakiltar Hausawa da yaren Hausa.

2- Lokacin da Adnan ya saki matar sa Mubina, da kuma inda ta dawo gidan iyayen ta bayan ya saketa, muryoyin jaruman basu hau da bakunan su ba a wuraren. Har ila yau, sa’in da Nasir ya hadu da Halima bayan auren ta da Adnan, hirar da sukayi akan gargadin da yake jaddada mata na hana ta zaman lafiya da mijin ta, nan ma dai muryoyin su basu hau da bakunan su ba.

3- A farko-farkon fim din me kallo yaji Halima tana fadawa Adnan cewa auren su fa saura SATI BIYU, alokacin da take zaune a cikin motar sa sa’in da tayi masa korafin baya daukar wayar ta a gaban matar sa. Amma sai gashi kuma lokacin da Adnan yakai karar Mubina wajen mahaifiyar ta yana cewa auren sa saura WATA BIYU. Shin meye gaskiyar lamari a tsakanin fadar Halima na cewar saura sati biyu, da kuma shi Adnan a gaba da yace saura wata biyu? Idan kuma shi Adnan din ne ya yiwa mahaifiyar Mubina karya saboda wani dalili to ya dace a bayyana hakan.

4- Shin ya makomar Nasir (Nuhu Abdullahi) Tsohon saurayin Halima wanda yaci alwashin hana ta zaman lafiya idan ta auri wanin sa? Tun bayan auren Halima lokacin da aka nuna yazo yana jaddada mata mugun kudirin sa har fim din ya kare ba’a sake jin duriyar sa ba, shin hakura yayi ya fasa aiwatar da kudirin sa akan auren Halima ko kuma wani matakin aka dauka a kan sa? Ya dace a bayyana makomar yadda abin ya kasance.

5- Bayan Adnan ya saki Mubina me kallo yaga ta kira sa tana kuka ta sanar masa da cewar Halima ta bar ‘ya’yan ta sun tafi makaranta babu abinci, yayin da Halima ta karyata hakan sa’in da suka yi waya da Adnan, amma bayan sun gama wayar me kallo yaji Halima tana cewa ita ba baiwa bace bazata iya wahala da ‘ya’yan Mubina ba. Sai dai kuma an nuna cewar Halima kamila ce mai son zaman lafiya da kowa, shin canja halin ta tayi har take cuzgunawa ‘ya’yan Mubina? Tunda ba’a nuna wuraren da Halima ta cuzgunawa ‘ya’yan Mubina a aikace ba sai a baki da aka fada, ya dace a bayyana abin karara ta yadda mai kallo sai fahimci gaskiyar lamarin.

Karkarewa:

Fim din ya nishadantar ta hanyar nuna rikicin wasu matan wadanda suke gudun ayi musu kishiya, sannan kuma ya fadakar ta hanyar nuna cewar rikicin da wasu matan suke yi a lokacin da za’a yi musu kishiya, hakan baya sauya ra’ayin miji akan kudirin sa, sai dai ma hakan ya zamo silar lalacewar auren mata masu irin halin Mubina. Wallahu a’alamu!
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: