Connect with us

LABARAI

‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 700 Bisa Zargin Miyagun Laifuka

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa ta kama mutum 700 bisa zargin aikata miyagun laifuka. Wadanda rundunar ta kama sun ce; sun hada da mutum 424 bisa zargin yin garkuwa da mutane, sannan da mutum 276 bisa zargin fashi da makami a fadin kasarnan.

Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya, Mohammed Adamu shi ne ya bayyana hakan a yayin wani zaman ganawa da ya yi da ofisoshi da masu mukamin Kwamishinoni a birnin tarayya Abuja.  Ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a tsakanin ranekun 1o ga watan Mayu zuwa 14 ga watan Yuni a jihohin Kaduna, Nasarawa, Katsina, Taraba, Kano da Edo.

Adamu ya ce sun samu wannan nasarar ne sakamakon atisayen ‘Puff Adder’ da rundunar ‘yan sandan suka kaddamar domin magance matsalolin tsaron cikin gida a fadin kasarnan.

Ya bayyana jihar Kaduna a matsayin jihar da ta fi yawan mutanen da aka kama, inda aka kama mutum 101 da ake zargi da garkuwa da jama’a, sai kuma jihar Katsina da mutum 79, sai Nasarawa da mutum 54 da Taraba da mutum 32.

Dangane da wadanda aka kama da fashi da makami kuwa, jihar Edo ke da yawan masu fashi da makami. Inda aka kama mutum 38 sai Nasarawa da mutum 25, sannan birnin tarayya Abuja da mutum 23.

Ya ci gaba da cewa; an samu ‘ammunition ‘ 10, 860 a daga hannunsu, sannan da bindigogi daban-daban guda 301 ciki harda roket da AK 47 da kananan bindiga da kuma bindigogin gargajiya.

Adamu ya ce jihar Katsina ke da adadi mai yawa na makaman da aka kama wanda ya kai 80, dai jihar Edo da 26 sannan Kaduna da 25.

Har wala yau ya ce sun kama mutum 176 wanda ake zargi da shiga kungiyoyin asiri a fadin kasarnan a tsakanin wannan watannin, a yayin da suka kama ababen hawa 77 daga hannunsu. Ya ce cikin wadannan watanni sun yi nasarar cafke mutum 44 da ake zargi da kisan kai inda mutum bakwai daga birnin tarayya Abuja, shida daga jihar Kano. Ya tabbatar da cewa sun samu wannan nasarar sakamakon jajircewar ‘yan sanda da kuma taimakon al’umma da sauran wadansu kayayyakin da suka taimaka musu.

Ya ce za su ci gaba da bunkasa atisayen ‘Puff Adder’ domin ganin sun ci nasarar kafa wannan atisayen. Ya tabbatar da cewa da jami’an ‘yan sandan cewa gwamnatin tarayya a shirye take wajen taimakawa rundunar ta su wajen magance matsalolin da suke fuskanta.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: