Connect with us

KASUWANCI

An Yi Asarar Kudin Jari Na Naira Biliyan 111 2018

Published

on

Kasuwar sayar da hannun jari ta kasa ta kara mastar da zamanta zuwa ranar alhamis bayan da aka samu aka tabka asarar shiya har ta naira biliyan 111 bayan faduwar farashi na na kayan da akayi akayi hada-hadar su a kasuwar a ranar talatar dta gabata.

Dukkan shiyar da kuma kasuwar an lissafa sun sauka zuwa kashi 0.88 bisa dari da ya kusa kaiwa 34,110.22 da kuma naira tiriliyan 12.452 baki daya. Har ila yau, sauran kididdigar sun sauka saboda ran da aka sanya akan mai da kuma iskar Gas harda ita kasuwar da ake sayar da kayan,inda suka hau zuwa kashi 0.15 bisa dari da kuma kashi 0.38 bisa dari baki daya, inda kuma kusuwar da kuma ASeM suka kulle ba tare samun komai ba. Farashin kaya talatin da daya suka durkushe, inda suka haura samada da ashirin da shida a ranar , inda kuma kaya guda sha tara suka kare farashinsu har ila yau, an samu kasa da shirin a ranar laraba.

Kididdigar fanin banki ta sauka da kashi 2.49 bisa dari haka bankin Diamond Bank Plc, Ecobank Transnational Incorporated, Fidelity Bank Plc, Guaranty Trust Bank Plc, da Jaiz Bank Plc duk sunyi asara. Bugu da kari, fannin Inshora kididdigarsu ta sauka zuwa kashi 0.21 bisa dari saboda asarar da kamfanin Inshora na AIICO Plc da Law Union da kamfanin inshora na Rock Plc, da kamfanin inshora na Mutual Plc, da kuma kamfaninb inshorwa na Niger Plc sukayi.

Har ila yau, kayan da masu saye suke saye sun sauka da kashi 1.06 bisa dari.

Kamfanonin da suke akan gaba da sukayi kokari sune, AG Lebentis Plc, Fidson Plc, kamfanin inshora na Sobereign Trust Plc, kamfanin Royal Edchange Plc, da bankin Unity Plc, wadanda suka samu riba har ta kashi 10 bisa dari da kashi 9.09 bisa dari, da kshi 8.70 bisa dari da kashi 8.33 bisa dari da kuma kashi 6.76 bisa dari. Wadanda kuma suke akan gaba wajen tabka asara sune, kamfanin Inshora na Wapic Plc, Eterna Plc, kamfanin Law Union, kamfanin irnshora na Rock Plc, kgamfanirn inshora na Standard Alliance Plc, da kuma kamfanin Unileber Nigeria Plc, wanda sukayi asarar kashi 10 9.42 da kshi 9.09 bisa dari da kashi 8.57 bisa dari da kuma kashi 6.40 bisa dari baki daya.

Jimlar shiya biliyan 1.147 data kai naira biliyan 12.546 da akayi hada-hadar kasuwanci na 16,649 da akayi kasuwancinsu a satin da ya wuce masu zuba jari suka zuba a kasuwar ta shinku sabanin jimlar shiya ta naira miliyan 925.630 da aka kiyasta ta kai naira biliyan 8.333 da suka shiga hannui a hada-hada 15,565 kafin satin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: