Connect with us

KASUWANCI

Zafi Ne Ke Janyo Tsadar Kayan Lambu, Cewar Shugaban Kungiyar Kayan Gwari

Published

on

Shugaban masu sayar da kayan gwari na jihar Gombe Alhaji Sani Waya, ya danganta samun ruwan sama mai karfin gaske da akayi, inda hakan ya sanya kasa ta yi zafi aka kuma samu lalacewar kusan kashi casa’in na kayan gwari da aka shuka a wasu ginakan dake cikin jihar ta Gombe.

Shugaba Alhaji Sani Waya ya bayyana hakan ne a hirar sa da Jaridar Daily Trust a a jihar ta Gombe.

A cewar shugabkn, yanzu haka suna samun tattasai ne daga kasar Nijar, Jihar Katsina, yayin da tumatir kuma suke sayo shi daga kasar Kamaru, sai yanzu ne tattasai da ake nomawa a Karamar Hukumar Balanga dake cinin Jihar ta Gombe, inda ya yi nuni da cewa, kayan ya fara samuwa, inda hakan yake nuna kayan zai iya yin sauki nan ba da dadewa ba.

Shugaban ya ci gaba da cewa, tunda farko abin da ya fara kawo tsadar kayan gwari shi ne ruwan sama mai yawa da aka yi, zafin da kasar ta yi ne ya haifar da lalacewar amfanin gonar sannan da rashin noma shi sosai kamar yadda aka saba a baya saboda tsoron yanayin da ake ciki kada a noma da yawa ya lalace.

Alhaji Sani ya kara da cewa, kayan ya yanke musu sai suka koma sayo shi daga garuruwan Jos da Katsina da kuma kasar Nijar.

Ya sanar da cewa, duk da yankewar da kayan ya yi yana da sauki a kan bara, domin a bara suna sayar da solon buhun tattasai a kan naira dubu 25 amma yanzu bai wuce naira dubu 17 ba.

Kwandon tumatir kuwa a bara naira dubu 13 zuwa 15 har dubu 17 sun sayar, amma yanzu haka tsadarsa naira dubu 8 har dubu 4 sun sayar a lokacin salla karama data wuce.

Shugaban ya sanar da cewa, Ita kuwa albasa, ba ta kara kudi ba a kan yadda suke sayar da ita a barar, inda solonta yana nan a kan naira dubu 6 zuwa dubu 6 da 500 zuwa dubu 7.

Shugaba Alhaji Sani Waya, ya ce kada mutane su dauka saboda lokacin Sallah ne da aka fi bukatar kayan suke kara tashi, amma dalilan da ya zayyana sune sume janyo tashin farashin na kayan gwari.

A cewar Shugaban, a shekarun baya daga nan Gombe har kasar Ghana da Kamaru suke shigar da kayan su amma yanzu saboda yadda ya yanke sai dai su ma su je Kamaru da Nijar su sayo, kuma a hakan da yake tattasai dan Balanga ya fara fitowa suna iya kaiwa jihohin Bauchi da Adamawa da Borno.

Ya yi kira ga sabuwar gwamnatin jihar ta kula da manoman kayan gwari kamar yadda gwamnatin baya ta yi nata kokarin.

A karshe Shugaban ya yi kira ga suma manoman da kada su yi kasa a gwiwa su kara himma wajen fadada noman don kauce wa tsadar kayan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: