Connect with us

WASANNI

Barcelona Za Ta Sayi Neymar Da Griezmann A Lokaci Daya

Published

on

Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana burin sayan Neymar Jr da kuma Antonio Griezmann a wannan kakar bayan da gaba daya ‘yan wasan biyu suka nuna sha’awarsu ta komawa kungiyar ta Barcelona da buga wasa.

A baya bayan nan dai, an sha alakanta Griezmann da komawa Barcelona, bayan da ya bayyana aniyar rabuwa da kungiyarsa a bana sai dai tun bayan da yace zai bar Atletico Barcelona bata yiwa kungiyar tasa maganar ciniki ba.

A shekara ta 2018 Barcelona ta yi kokarin siyan Griezmann amma yayi watsi da tayinta yayinda tsohon kociyan Manchestet United ma Jose Mourinho yaso siyan dan wasan amma Griezman yaki amincewa yabar Atletico a shekara ta 2017.

Tun bayan da Neymar yabar kungiyar ta Barcelona aka fara rade tadin cewa Barcelona zata iya komawa domin sake sayansa saboda dan wasan baya jin dadin zaman kasar Faransa kuma ya fara da na sanin barin kungiyar ta Barcelona.

Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta shirya sayar da dan wasan kuma itama kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tana bukatar sake komar dashi sai dai farashin dan wasan ne zai yiwa Barcelona yawa.

Sai dai kawo yanzu Barcelona tana fatan sayan ‘yan wasan guda biyu gaba daya domin tunkarar kakar wasa ta gaba bayan da ta shirya rabuwa da wasu daga cikin ‘yan wasanta domin samun kudin siyan wadannan ‘yan wasa.

Idan har Barcelona tana son siyan Neymar da Griezman tana bukatar ta siyar da manyan ‘yan wasanta da suke kasuwa a yanzu da suka hada da Iban Rakitic wanda Manchester United take zawarci sai Phillip Coutinho da kuma dan wasa Ousmane Dembale wanda Liverpool da Arsenal suke zawarci kuma shine tun farko Barcelona ta sayo domin maye gurbin Neymar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: