Connect with us

ADABI

Tasirin Wakokin Mata Ga Wadanda Aka Yi Ma Su Na Dokta Mamman Shata Katsina (3)

Published

on

Mata Masu Alaka Da Sana’a 

Babayaro (2003) da Modibbo (2013) sun  nuna cewa saboda farin jinin makadin, galiban wadansu mata tun suna kanana Allah ke dora masu son Shata da wakokin sa (Hauwa ‘Yar Bori, 1998; Munari, 2000; Jamila, 2002; Munari, 2007) Wadda duk makadin ya yi ma waka sai ka tarar dama can tun tana karama ta ke son wakokin sa (Ali Kwado, 2011; Koko, 2014) A wannan ajin, an samu zantawa da mata kamar:  Hajiya Asibin Danmusa (1973) da Hajiya Hauwa mai tuwo (1976) Kululu ta nuna cewa duk irin nasarar da Dan Adam ke tunani mahaluki za ya iya samu a rayuwa to ita ta samu ta dalilin wakar da Shata ya yi mata. Tun tana da shekara goma ta ke son wakokin makadin. To a cikin 1976 a Kano ta sanya Ahmadu ministan roko ya yi mata hanya zuwa ganin makadin a gidan sa da ke unguwar Kurnanr Asabe (Hauwa, 1998)

Hauwa ta yi sa’a cewa Shata ya yi amfani da wakarta ya yi ma wasu abokan hamayyar sa ta siyasa gugar zana, da ya ke abin ya zo daidai kan wannan gabar. Wannan ya sanya ma wakar ta ta yi nisa.

Abin da ya fi birge Hauwa ga wakarta shi ne martanin da ya mayar ma wata mata makwabciyar ta mai sayar da abin ci daidai da yanda ta ja ta fada. Wayyawoniya Allah, ‘yan birni kun iza ni kun gaza fidda ni/

Amma ita Assibin Danmusa duk da ya ke mahaifinta Idi mai tarko ya yi tarayya da Shata saboda kasancewar su mahalba duk yunkurin a yi hira da ita sai ba ta amince ba, illa iyakaci idan an je bincike ta yi dariya ta ce ‘ai wannan abin ya wuce, a yi hakuri’. Amma ta bayyana cewa wakar Shata ta sanya sana’ar abincin ta ta kara daraja da farin jini. Kumai ta kadai ce Shata ya kira ta ‘gajera’ a wakar ta, duk da cewa da gaske gajerar ce, kuma baka.

Mata Masu Alaka Da Siyasa/Zaman Kai

Mata masu kasaita ko zaman kan su ba za su saki jiki su bata lokaci su fadi labarin sana’ar su ba amma suna iya bada labarin sababun da ma tasirin wakar su (Tambaya, 2003; Indo, 2008; Assibi, 2005; Ajeje, 2012) Wannan shi ne tarkin da aka samu. Indo Musawa ce da Maimuna Munari kurum suka saki jiki suka bayar da tarihin yadda aka yi har ma suka fito yawo (Rediyo Kebbi, 2014)

Sai kuma ga zamanin Siyasar NPC da NEPU wanda ‘yan siyasa dole su ka nemi gudunmuwar mata don su taimaka masu wajen yi masu kamfe ga mata ‘yan uwan su don su ci zabe (Tambaya, 1998; Indo, 1998). Don hakane ma a kowacce shiyya ta Nijeriya, ba ma dai Arewa aka shiga nada mata shuwagabannin NPC a Lardunan su. Wasu matan da suka shahara a karkarun su ko ma garuruwan su da suke basu isa su dauki gurbin zama shuwagabannin NPC ko NEPU ba suma Shatan ya yi masu waka, kurum ma don sun yi wa jam’iyyu hidima. To shaharar ta sa su ke da dan abin hannun su da har Shata na iya waiwatar su ya yi masu kirari. (Boube, 2013) Hauwa-Sokoto, 2016)

A wannan ajin akwai Hajiya Amina Tambaya ‘Yar Mu’azu Zariya (1943) da Hajiya Maimuna Munari (1962) da Hajiya Indo ‘Yar Mamman Pindiga (1966)

Tambaya ta san makadin tun cikin 1943 sa’ilin da ya fara ziyartar Zariya, ya je bukin Shehu kanen Umaru Tulu wan Mammada. Ko da ya je a lokacin, ya tarar tana da gidan mata a titin Alkali, Tudun wada Zariya. Ta bayyana cewa wakokin ta da kuma tarayyar su sun dada sanyawa sunan ta ya kai duk inda ba a ma zato. Sunan ta ya bazu kamar wutar bazara saboda Shata.

A gidan Dutse na Funtuwa wani fitaccen gida na mata masu zaman kan su mallakar Shatan Debis, wata mutumniyar Kafanchan (ta rasu cikin Fabrairun 1972), tun kafin Kasar nan ta samu ‘yanci, watau cikin 1958 Munari ta gudu daga gidan aure ta zo Funtuwa tana yi wa wata Magajiya mai sayar da tuwo da naman kaji wanke-wanke,daga baya da ta goge sai ta koma gidan Dutse da zama. To bayan Shata ya koma Funtuwa da zama cikin 1960/61 a kullum dare ana hira sai Shata ya ji ana cewa ‘Munari gidan Dutse’Amma bai taba ganin ta ba. Sai rannan ya yi mata takakka, ya shiga gidan ya nemi ya ganta. Aka kira masa ita, suka gaisa. Ya ce mata dama bai taba ganin ta ba amma ya ji ana yawan fadin ta a cikin kwaryar Funtuwa.  Wakar makadin ta kara mata farin jini da yawan masoya a tu daga Funtuwa har Kano, har Legas, har ya zuwa Maiduguri. Domin kwarjinin wakar ne ma aka sanya ta ta zama jigo a NPC a nan Funtuwa. Ya kan ce: In don lemu da abarba da biredi akwai su a Funtuwa Mairo Munari/ Watarana ne yana daga cikin mota suna gaisawa da Mairo a kusa da Gidan Dutse sai wani direba ya isa Funtuwa daga Kano, ya mika mata tsarabar su abarba din. Sai ta gwalashe shi, ta ce ‘yau biredin banza, duk gas u nan Funtuwa ana sayarwa, wannan tsarabar har kokari ka yi? Jin haka, sai makadin ya fashe da dariya. Dalilin ambaton wannan baitin ke nan.

Ita A’I Pindiga ta fara ganin sa cikin 1966 da ya tsaya Gombe a kan hanyar sa ta komawa gida daga bukin nadin Sarkin Jalingo. Da dare ya yi wasa a kofar gidan Sarki. Sai suka shiga hamayya, ita da Umaru Ciroman Gombe wajen ba shi kyauta. A rannan ya yi mata waka. Wanshekare ta bi su suka komo Funtuwa tare. Kai, Indo ce saboda tsananin son Shata da son wakar da ya yi mata ta bi shi har Legas da Kano da Maiduguri. Da makadin ya ga ba ta da niyyar komawa gida sai ya sallame ta ya ce ta yi hakuri ta koma gida kada ta biye masa. Sai mazan kwarai sun zauna, muddin mazan kwarai sun zauna, in ga halin Indo ‘yar Mamman/  Indo ta ce a lokacin ita ce mai fadi a ji a cikin matan NPC duk fadin kasar Gombe. Ko namiji dan gidan sarauta ba ya iya ja da ita, don ta fi shi. Shi ya sanya makadin ya fadi haka.

Makadin ya yi ma Yalwar Shandam wakoki biyu a Kano, masu fasalin Hakananne Mamman Kanen Idi Wan Yalwa,  sai kuma wata daban da ya kan ambace ta a cikin wakar Yakubi Shandam (Yalwa, 2015; Labaran, 2018)
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: