Connect with us

KASUWANCI

An Tura Naira Tiriliyan 1.26 A Asusun Gwamnatin Tarayya A 2018 – NNPC

Published

on

Kamfanin NPPC ya sanar da cewa, yatura naira tiriliyan 1.26 a cikin asusun Gwamnatin Tarayya.

Kamfanin ya sanar da hakan ne a a ranar talatar data wuce a cikin sanarwar day a fitar a garin Abuja.

Daraktan sashen kudi na kamfanin, Mista Godwin Okonkwo ne ya sanar da hakan a cikin sanarwar day a fitar.

Mista Godwin Okonkwo ya ci gaba da cewa, lissafa wadansu hanyoyi biyu da kamfanin ya bi wajen tura kudaden zuwa cikin asusun naGwamnatin Tarayya sun hadada, ta hanyar hada ka da kamfanoni hakar mai wajen sayar da danyen mai da kuma wanda ake sayar da shi cikin gida.

Ya ce, su na bin hanyar da ta da ce wajen sanya kudaden hada kar a cikin asusun Tarayya.

Ya kara da cewa kamfanin yana yin taka tsantsan wajen kashe kudaden hakar mai da iskar gas don gujewa tabka irin kuskuren baya, inda ya yi nuni da cewa, halin da harkar mai ke ciki yanzu a krasa nan, hali ne na nasara ga ci gaban kasa.

Ya ce, NNPC ya na bin wasu matakai na tara kudaden shiga domin ci gaban kasa kuma kaucewa hanyoyin ficewar kudede ba a bisa ka’ida ba.

Ya kara da cewa, kamfanin yana duba litaffin shigar da kudi zuwa asusun Tarayya lokaci zuwa lokaci domin tabbatar ba’a gadar da bashi ga ’yan kasa ba.

Yayi watsi da zargin da wasu kwamishinonin kudi suke yiwa kamfanin na NNPC cewa bai sanya wasu kudade a asusun Tarayya ba cikin shekara 2017 zuwa Disambar 2018.

Ya jadda cewa, kamfanin yana bin dukan ka’idar kudi tare da masu ruwa da tsaki.

Ya yi nuni da cewa, zuba jari a harkar iskar gas da fetur tana daukar lokaci ka fin ta kai ga gaci.

Ya ce, idan NNPC yaki sanya jarin da ya dace, nan gaba, ba baza a samu kudin da za ta raba wa rukunin Gwamnati guda ukkun da mu ke da su ba.

Da a ka tambaye shi ga me da ko NNPC ta sanya kudaden harajin 2018, yace a cikin watan gobe NNPC zai fitar da Jadawalin kudaden da ya tara kuma za a tura su zuwa cikin asusun Tarayya.

Ya ce NNPC ya yi bayani a kan duk wata takaddama ta kudade na shekarar 2018 kuma yin bayanin abin da ya jawo tsaiko.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: