Connect with us

WASANNI

Eriksen Ya Na Son Koma Wa Manchester United

Published

on

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Cristian Eriksen ya bayyana aniyarsa ta komawa Manchester United bayan da kokarin da yayi na komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bai samu ba.

Siyan dan wasa Edin Hazard da Real Madrid tayi da kuma neman da kungiyar take yiwa dan wasan Manchester United Paul Pogba shine yasa kungiyar taja baya wajen neman dan wasan na Tottenham wanda kwantiraginsa zai kare nan da watanni 12 a kungiyar.

Sai dai kawo yanzu dan wasan dan asalin kasar Denmark yana fatan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zatayi kokarin ganin ta sayeshi domin ya koma kungiyar yayinda itama kungiyar kwallon kafa ta Juventus take cigaba da zawarcinsa.

Dan wasan mai shekara 27 a duniya ya zura kwallaye 10 a raga sannan kuma ya taimaka an zura guda 17 acikin wasanni 51 daya bugawa Tottenham inda kuma kungiyar taje har wasan karshe na kofin zakarun turai sai dai sunyi rashin nasara a hannun Liverpool.

A kwanakin baya dai dan wasan ya bayyana cewa lokaci yayi da zai bar Tottenham domin komawa wata kungiyar sai dai shugaban gudanarwar kungiyar ta Tottenham ya bayyana cewa yana fatan cigaba da zaman dan wasan a birnin na Landan.

Eriksen dai ya shafe shekara shida a kungiyar Tottenham bayan daya koma kungiyar daga Ajad ta kasar Holland kuma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce kungiyar data dade tana zawarcin dan wasan wanda ya bugawa kasarsa ta haihuwa Denmark wasanni da dama.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: