Connect with us

WASANNI

Mun Sadaukar Da Nasararmu Ga Samuel Kalu

Published

on

Kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeriya, John Obi Mikel, ya bayyana cewa sun sadaukar da nasarar da suka samu akan dan wasa Super Eagles, Damuel Kalu bayan da dan wasan ya fadi a lokacin da ake tsakiyar daukar horo.

An dai garzaya da dan wasan tawagar kwallon kafar ta Najeriya, Samuel Kalu zuwa asibiti, bayan da ya fadi a lokacin atisayen tunkarar karawa da Burundi a gasar kofin Afirka wanda aka fara a ranar Juma’a.

Dan kwallon mai shekara 21, mai buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Bordeaud ta kasar Faransa ya fadi ne a wajen atisaye a ranar Juma’a sai dai likitocin tawagar ta Super Eagles sun bashi taimakon gaggawa kafin kuma a garzaya asibiti.

Najeriya ta buga wasan farko a rukuni na biyu da kasar Burundu wadda karon farko kenan ta fara buga wasannin a yanayin zafi da ake cewar zai kai 40C (104F) a filin wasa na Aledandria dake kasar ta Masar.

“Samuel Kalu dan uwanmune kuma muna masa fatan samun sauki cikin gaggawa saboda haka mun sadaukar da nasarar da muka samu akansa saboda dan wasane jarimi wanda zai taimakawa tawagar idan har yasamu lafiya” in ji Obi

Hukumar kwallon kafar Afirka, Caf ta tsara cewar za a dinga yin dan takaitaccen hutu har karo biyu, domin bai wa ‘yan wasa damar shan ruwa kamar yadda dokar Fifa ta amince kuma kowanne wasa za a yi hutun minti uku a minti na 30 da fara wasa da kuma minti na 70, domin bai wa ‘yan kwallo damar shan ruwa da kuma goge zufa.

Wannan ne karon farko da za ake buga wasannin cin kofin Afirka tsakanin Yuni da Yuli, inda aka yi hasashen cewar yanayi na zafi a Masar ya dan yi sama zai kuma ci gaba da zama a hakan zuwa watan gobe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: