Connect with us

LABARAI

Sabon Fasfon Nijeriya Zai Dakile Ayyukan Bata-gari, In Ji Shugaban NIS

Published

on

‘Yan Nijeriya masu mummunan kuduri yanzu zai yi musu wahala wajen samun sabon fasfon kasar mai dauke da wa’adin shekara goma, domin yanzu yana dauke da sama da lambobin tsaro ashirin da biyu kamar yadda hukumar shige da fice ta kasa wato NIS ta bayyana.

Babban Konturola din hukumar, Muhammadu Babandede shi ne ya bayyana hakan a yau a yayin kaddamar da sabon fasfo din a ofishin hukumar dake garin Ikoyi, inda ya ce yanzu abu ne mawuyaci bata gari da suke da mummunan manufa su yi aiki da sabon fasfo din domin yanzu yana dauke da lambar sirri ta zama dan kasa wato NIN da kuma lambar sirri ta Banki wato BVN. A cewar Babban Konturolan, kafafen watsa labarai na nuna cewa; sabon Fasfo din na da wahala wajen samunsa, wanda ya ce; wannan batun sam ba haka yake ba.

Inda ya kara da cewa; “Dole ne masu mummunan kuduri da suke son sabon Fasfo din su koka. Domin sabon takardar fasfo din za a hada shi da lambar sirri ta zama dan kasa wato NIN da lambar sirri ta Banki wato BVN. Ya kamata ‘yan Nijeriya su yi amfani da shaidarsu ne a duk lokacin da suka bar kasarnan ne, ba wai idan sun bar kasar su canza sunayensu domin aikata wadansu ayyukan ba.” In ji shi.

Ya ci gaba da cewa; sabon fasfo din yana nuna dunkulewarmu ne a matsayin mu na ‘yan Nijeriya, kuma zai taimaka wajen bunkasa ci gaban zamantakewa, tattalin arziki. Sannan ya ce; abu muhimmi shi ne mawuyaci ne yanzu mutum ya iya sauya bayanan da ke cikin sabon fasfo din. Inda ya kara da cewa; ya kamata ‘yan Nijeriya su sani cewa; “ba za mu iya sauya bayanan bankinsu ba da zarar sun ba da, a don haka ya kamata su kwana da shirin sanin haka.” In ji shi.

Da yake karin bayani dangane da yiwuwar samun Fasfo biyu domin amfani da su, shugaban hukumar NIS din ya yi tir da wannan yunkurin, inda ya kara da cewa; “mun kama ire-irensu da dama har a nan Legas a filin jirgin sama. Za su ce sun batar (ko an sace musu) Fasfo dinsu, sai a yi musu sabo, sai kuma su dawo suna amfani da wanda suka ce ya bata din ko an sace. Mun kama ire-irensu, sai su rika ba da uzuri daban-daban, ba su san cewa a duk lokacin da ka ce fasfo dinka ya bace ko an sace ba, muna sanya shi cikin alama, da zarar ko waye ya yi amfani da shi a ko’ina, za a kama wannan mutumin kuma zai fuskanci hukunci.” Ya tabbatar.

Shugaban hukumar ya kaddamar da ayyuka takwas wadanda masu hulda hukumar NIS da masu ruwa da tsaki suka gina. Cikin ayyukan da aka kaddamar harda cibiyar SERVICOM wacce aka gina tare da hadin guiwar Bankin Heritage, da kuma mota kirar Bas mai mazaunai goma sha takwas, wanda Bankin Fidelity suka bai wa ofishin hukumar NIS din dake garin Ikoyi. Sannan da wani katafaren gini da hukumar lura da tasoshin ruwa wato NPA suka ba su.

Sauran sun hada da; wani gini da aka yi a cikin harabar wurin, domin lura da sauya suna wanda Bankin Zenith suka gina. Da kuma wurin da masu shigar da korafi za su rika tsayawa da Bankin Access suka gina. Sai sabunta dakin sanya sunaye da Still Earth Capital suka gyara. Da kuma dakin taro da Bankin GTB suka gina.

Da yake karin bayani dangane da wadannan ayyuka, shugaban NIS din, Babandede ya ce wannan huldar da ke tsakanin hukumar da wadannan kamfanunnuka, ya nuna cewa bangaren da ba na gwamnati ba da gwamnati za su iya aiki tare. Ya ce; akwai bukatar a yi koyi da wadannan kamfanunnuka masu zaman kansu musamman a bangaren lura da kayayyaki. Ya ce; suma har wala yau kamfanunnukan za su iya koyi da su.

Da yake na sa martanin, wakilin Bankunan, Amaechi Okobi, wanda shi ne jami’in sadarwa na Bankin Access ya ce; Bankunan za su ci gaba da bada hadin kai ta fuskacin kirkire-kirkire, sannan za su ci gaba da ba da hadin kai a duk lokacin da bukatar hakan ta ta so. Inda ya ce; “zamu ci gaba da ba da hadin kai domin ci gaban sashen da ke kula da kostomomi wato CRS a takaice. Ba za mu dogara da gwamnati ba a matsayinmu na masu zaman kan su, a duk lokacin da kuke da bukatarmu, ku ka kira mu, zamu kasance a wurin.” Ya tabbatar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: