Connect with us

LABARAI

Ana Tuhumar Tsohuwar Gwamnatin Bauchi Da Kashe Biliyan Biyu Domin Jana’iza

Published

on

Gwamnatin Bauchi a karkashin Sanata Bala Mohammed ta ce, tsohon Gwamnan jihar, Mohammed Abubakar ya kashe Naira biliyan 2 da miliyan 300 wajen saya wa mamata likkafani da wasu kayayyakin jana’iza cikin wata biyar kacal.

Kakakin gwamnan, Dk. Ladan Salihu ya shaida wa manema labarai cewa, an kashe kudaden ne tsakanin watan Janairu zuwa Mayun shekarar bana. Dk. Salihu ya ce, an kashe sama da Naira miliyan 900 wajen sayen likkafanin mamatan, yayin da aka kashe Naira biliyan 1 da miliyan 400 wajen sayen katakon da ake shimfidawa a cikin kaburbura.

Sai dai tsohon Gwamnan ya musanta zargin wanda ya bayyana a matsayin abin dariya, amma gwamnati mai ci ta ce, tana da shaida akan batun. Gwamnatin jihar ta kuma kara da cewa, za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an maido da kudaden talakawan jihar da aka wawure.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: