Connect with us

LABARAI

Kotu Ba Ta Yi Watsi Da Bukatana Kan Hukumar Zabe Ba –Atiku

Published

on

Dan Takarar Shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa, ba ta yi watsi da bukatar da ya shigar mata ba, na neman bincika turakar ajiyar bayanan intanet na hukumar INEC.
Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a bayan da hadimin Shugaban kasa a bangaren watsa labarai ya bayyana hukuncin kotun a matsayin “Nasarar da aka samu akan farfaganda”.
‘Bukatar da Atiku ya shigar, inda suka bukaci kotu ta basu damar bincika tukarar ajiyar intanet na hukumar INEC, kotu ba ta yi watsi da bukatar ba.’ inji Paul Ibe
A karshen bangaren Atikun sun bayyana cewa, komai daren dadewa gaskiya za ta yi nasara a kan karya, don haka duk masu murna su ma daina murna, saboda ba a kawo karshen wannan lamarin ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: