Connect with us

RIGAR 'YANCI

Masarautar Agaie Ta Yaba Wa Gwamnatin Neja Bisa Nada Mace Shugabar Ma’aikata

Published

on

Masararautar Agaie ta yaba wa gwamnatin Neja kan bai wa Hajiya Salamatu Abubakar mukamin shugaban ma’aikatan gwamnati, musamman ma don kasancewar ta ’yar asalin yankin masarautar.

Yabon ya biyo bayan ziyayar godiya da tawagar masarautar a karkashin jagoracin Sarkin Agaie, Mai Martaba Alhaji Yusuf Nuhu, ta kawo wa gwamnan a fadar gwamnatin jihar da ke Minna a karshen mako.

Gwamnan Abubakar Sani Bello ya bada tabbacin bai wa mata gurabe a cikin gwamnatinsa a kudurinsa kafa gwamnati mai adalci wadda za ta kau da bambamcin jinsi a cikin gwamnatinsa wanda zai baiwa kowa damar bada tashi gudunmawa dan samun gwamnati mai adalci duba da irin rawar da suka bada wajen ganin gwamnatin ta dawo karo na biyu akan karagar mulki.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke karbar tawagar masarautar Agaie da su ka kawo ma sa ziyarar goyon baya a ofishin shi da ke fadar gwamnatin jihar da ke Minna.

Ya ce, zaben Hajiya Salamatu T. Abubakar ya biyo sakamakon kwamitin da aka kafa dan samun wanda zai dare a wannan kujerar, duba da kwarewarta da jajircewarta akan aikin gwamnati yasa wannan kwamitin zakulo sunan ta inda nan ta ke gwamnati ta amince da wannan sakamakon.

Gwamnan ya ce, a matsayinta na mace ta farko da ta samu damar rike wannan kujerar ya biyo bayan gudunmawar da ta bayar a lokacin da ta rike mukamai da dama a jihar a bangaren aikin gwamnati, wanda ta taka rawar ganin da ya kai ga samun nasarori a aikin gwamnati wanda ya nuna wakilcinta a matsayinta na mace ta zama jakadiyar mace da ta fitar da mata kunya.

Gwamnan ya jawo hankalin mutanen Agaie da jihar ta Neja da su bai wa sabuwar shugaban ma’aikatan jihar goyon baya dan samun nasarar aikin da aka dora mata wanda zai ba ta damar daukaka darajar aikin gwamnati da ma’aikatan jihar.

Da ya ke bayani a madadin tawagar masarautar, Mai martaba Sarkin Agaie, Alhaji Yusuf Nuhu, ya yaba wa gwamnan bisa bai wa Hajiya Salamatu matsayin shugaban ma’aikatan jihar wadda ‘yar asalin masarautar ce.

Sarkin ya cigaba da cewar baiwa Hajiya Salamatu T. Abubakar matsayin shugaban ma’aikatan jihar wanda shi ne irinsa na farko ya nuna kudurin gwamnatin jihar na inganta tsarin aikin gwamnati a jihar wanda manufa ce mai kyau da ke nuna cewar gwamnati ta zo da kudurin gyare-gyare na tafiya da kowa a harkokin gwamnati ba tare da nuna bambamcin jinsi ba ta hanyar ta tafiya da kowa a harkokin gwamnati wanda wannan tsarin ne zai daga darajar gwamnati da samun gwamnati mai inganci a jihar.

Alhaji Yusuf Nuhu ya yabawa mai girma gwamna akan kudurinsa na adalci a manufarsa na tafiyar da tsarin shugabanci bisa tsarin siyasa mai adalci a jihar.

Don haka ya bai wa gwamnan tabbacin bada shawarwarin ga sabuwar shugabar da goyon bayan jama’arsa ga muradun gwamnati a kowani lokaci da zai tabbatar shugabanci na gari da zai inganta muradun gwamnati wanda zai kai ta a mataki na gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: